Yan bangan siyasa sun harbe kananan yara guda biyu a yayin gangamin siyasa
A ranar juma’a, 13 ga watan Disamba ne yayan jam’iyyar APC suka gudanar da wani gangamin siyasa a garin Bini na jahar Edo inda aka samu hatsaniya da yayi sanadiyyar jikkata kananan yara guda biyu.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito yaran sun samu rauni ne a sakamakon harbin mai kan uwa da wabi da wasu yan bangan siyasa suka bude a yayin da ake tsaka da yayan jam’iyyar APC magoya bayan tsohon dan takarar gwamnan jahar, Ize Iyamu suke kan hanyarsu ta zuwa gidan dan siyasar.
KU KARANTA: Boko Haram sun kwace motocin Sojoji makare da makamai, sun kashe mutum 14
Majiyar Legit.ng ta ruwaito ba wai yaran suna cikin gangamin yan siyasan jam’iyyar APC bane, a’a, gangamin ya hade ne da daidai lokacin da iyayensu suka aikesu, ashe tsautsayi na kansu, fitarsu keda wuya, harbin ya rutsa dasu. Yaran sune; Ovbiagele Ohimai dan shekara 7 da Joshua Samuel dan shekara 11.
A yanzu haka an mika su zuwa wani asibiti dake garin Bini, inda suke samun kulawa. Sai dai baya ga kananan yaran, akwai magoya bayan Ize Iyamu da dama da suka samu rauni daban daban a dalilin wannan harbin mai kan uwa da wabin.
A wani labarin kuma, mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kashe mutane 14 tare da jami’in rundunar Yansandan Najeriya guda daya a wani samame da suka kai jahar Borno dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru na AFP.
Wasu daga cikin matasa yan sa kai ne suka tabbatar da lamarin, inda suka ce yan ta’addan ISWAP ne suka kai harin a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba a cikin motocin yaki fiye da guda 12 a kauyen Mamuri dake jahar Borno.
Wani matashin sa kai, Babakura Kolo yace: “Sun kashe mana mutane 14 da wani jami’in dansanda, da misalin karfe 8 na dare suka kaddamar da hari a kanmu a cikin motocin yaki guda 14, inda muka kwashe awanni muna fafatawa. Daga karshe makamanmu suka kare, don haka Boko Haram ci galaba a kanmu.”
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng