Ke duniya! Uwargida ta hada baki da kwartonta sun kashe mijinta

Ke duniya! Uwargida ta hada baki da kwartonta sun kashe mijinta

Wata babbar kotun jahar Edo dake zamanta a garin Bini ta yanke ma wani kwarton Fasto da farkarsa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kamasu da laifin kashe Mijinta, Injiniya Victor Gabriel, ma’aikaci a hukumar man fetir na Najeriya, NNPC.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matar mai suna Eniobong Isonguyo ta hada baki ne da Faston cocin da suke zuwa tare da mijinta, mai suna Udoka Ukachukwu, inda take bashi dama yana saduwa da ita, har ta kai ga ya dirka mata ciki.

KU KARANTA: An gano gawarwakin Hausawa yan canjin dala da aka kashe a jahar Legas

Sakamakon bayyanar cikin da Fasto Udoka ya dirka ma uwargida Eniobong ne yasa suka yanke shawarar kashe Maigidanta domin kada ya gano aika aikan da suke aikatawa da juna a bayansa, kamar yadda Dansanda mai shigar da kara ya bayyana ma kotu.

“Matar da kanta ta fada ma Faston ya tsaya akan hanyar da Mijinta ke bi zuwa wajen aiki, don ya rage masa hanya, haka kuwa aka yi, Faston ya tsaya akan hanyar Sapele zuwa Bini har Mijinta ya tarar dashi, kuma ya daukeshi da nufin rage masa hanya.

“Suna cikin tafiya sai Faston ya dauko wani karfe daya boye a jikinsa ya buga ma mutumin a wuya, sa’annan ya tsayar da motar, ya kwashe man fetir dake cikin motar gaba daya, sa’annan ya yayyafa masa fetirin ya cinna masa wuta, da haka ya babbakashi ta yadda babu mai iya gane shi.” Inji Dansandan.

Bayan Faston da matar sun tafka wannan danyen aiki ne kuma sai kuma koma kan dukiyar mamacin suka shiga cin duniyarsu da tsinke, amma daga bisani dubunsu ta cika, inda aka daure matar, kuma ta haifi yaron Faston a gidan Yari.

Daga karshen zaman na ranar Alhamis, Alkalin Kotun, mai shari’a Geraldine Imadegbelo ta bayyana gamsuwarta da hujjojin da bangaren masu kara suka bayyana, don haka ta yanke ma Faston da Matar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel