Buba Galadima Ya ‘Gano’ Shirin Tinubu da Gwamnoni a Kafa Yan Sandan Jihohi

Buba Galadima Ya ‘Gano’ Shirin Tinubu da Gwamnoni a Kafa Yan Sandan Jihohi

  • Jigon NDC, Buba Galadima, ya yi magana game da shirin kafa yan sandan jihohi wanda ake ta ce-ce-ku-ce a kai
  • Buba Galadima ya gargaɗi cewa kafa 'yan sandan jihohi na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya da haɗin kan Najeriya
  • Ya yi nuni da yadda aka yi amfani da 'Native Authority Police' a baya wajen danniya, yana gargadin cewa irin wannan na iya maimaituwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jigo a jam'iyyar NDC, Nuna Galadima ya yi gargaɗi kan shirin kafa rundunar 'yan sandan jihohi a fadin Najeriya baki daya.

Buba Galadima ya bayyana cewa hakan na iya haifar da amfani da ita wajen siyasa tare da barazana ga haɗin kan Najeriya.

Buba Galadima ya soki shirin kafa yan sandan jihohi
Shugaba Bola Tinubu da jigon NDC, Buba Galadima. Hoto: Bayo Onanuga, Kwankwasiyya Reporters.
Source: Facebook

Da yake magana a wata hira da Arise TV, Galadima ya ce ba a fara tunanin kafa 'yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro ba.

Kara karanta wannan

ASUU ta koka kan rashin cika alƙawari, ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami'o'i 11 a Najeriya

Yan sandan jihohi: Buba Galadima ya zargi Tinubu

Buba Galadima ya yi zargin cewa Bola Tinubu da gwamnonin jihohi na neman kafa rundunar ne kafin zaɓe domin amfani da ita wajen kai farmaki ga 'yan adawa, tayar da hargitsi a zaɓe da kuma raunana dimokuraɗiyya.

Ya tuna da tarihin 'Native Authority Police' a Arewacin Najeriya, inda ya ce an yi amfani da rundunar wajen cafke da tsare 'yan adawa da zarge-zarge daban-daban lokacin zaɓe.

Ya kuma yi zargin cewa yadda aka yi amfani da rundunar a wancan lokaci ya sa mutane da dama suka tsere daga jihohin Kano da Katsina domin tsira da rayukansu.

Ya ce:

"Ba wanda ya fara tunanin kafa 'yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro. Idan rundunar 'yan sandan Najeriya da sojojin Najeriya ba za su iya shawo kan matsalar tsaro a ƙasar ba, to ina mamakin yadda 'yan sandan jihohi za su iya yin hakan.
"Abin da muka sani shi ne cewa Shugaban Ƙasa da gwamnoni na neman kafa 'yan sandan jihohi ne kafin zaɓe domin su yi amfani da su a matsayin ƙarfin siyasa wajen kai hari kan 'yan adawa."

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana babban abin da ke hana Arewa ci gaba

Buba Galadima ya zargi Tinubu, gwamnoni kan yan sandan jihohi
Jigon NDC, Buba Galadima yana jawabi da Rabiu Kwankwaso a gefensa. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Fargabar Buba Galadima kan yan sandan jihohi

Buba Galadima ya ƙara da cewa idan aka kafa 'yan sandan jihohi, akwai yiwuwar wata ƙabila ko addini su mamaye aikin ɗaukar ma'aikata, wanda zai ƙara rarrabuwar kawuna da rashin amincewa tsakanin al'umma.

Sai dai batun kafa 'yan sandan jihohi na ci gaba da jawo muhawara, inda masu goyon baya ke cewa zai inganta tsaro, yayin da masu adawa ke nuna fargabar amfani da shi wajen siyasa da take haƙƙin ɗan Adam.

Abin da dokar yan sandan jihohi ta kunsa

Mun ruwaito muku cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da dokar kafa ‘yan sandan jihohi bayan matsin lamba mai ƙarfi daga gwamnoni da kuma ƙaruwar matsalolin tsaro a ƙasar

Dokar ta sauya tsarin jami’an tsaron ƙasar ta hanyar maye gurbin sunan 'yan sanda domin samar da tsarin aiki da ya fi karkata ga fararen hula.

An samar da tsarin kuɗi guda biyu da kuma matakan gudanarwa domin tabbatar da ‘yancin gashin kai ta fuskar kuɗi da hana amfani da ‘yan sanda a harkokin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.