Rigima na neman raba ‘Ya ‘yan PDP daf da zaben Shugabanni a Edo

Rigima na neman raba ‘Ya ‘yan PDP daf da zaben Shugabanni a Edo

An samu sabani a tsakanin ‘Ya ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP, yayin da ake shirya zaben shugabannin jam’iyya a Watan Junairun nan.

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa wasu ‘Ya ‘yan PDP a karkashin PDP Youths for Justice sun yi barazanar jan-daga daga uwar jam’iyya.

Wannan kungiya ta ce za ta gudanar da zaben shugabanninta dabam idan har shugaban jam’iyya na jihar Edo, ya murde sabon zaben da za ayi.

Sanata Odion Ugbesia da Fred Okah ne aka tunanin za su nemi kujerar Dan Orbih wanda zai sauka a farkon bana, don haka aka fara shirin zabe.

Matasan PDP da ke karkashin lemar PDP Youths for Justice, sun zargi Dan Orbih da yunkurin kakaba Odion Ugbesia a matsayin Magajinsa.

KU KARANTA: Manyan APC a Imo sun ce Ministan Buhari ya na tare da PDP

Rigima na neman raba ‘Ya ‘yan PDP daf da zaben Shugabanni a Edo
PDP Youths for Justice ta ce APC na iya lashe zaben Edo 2020
Asali: Depositphotos

Shugaban wannan tafiya mai suna Musa Kadiri shi ne ya ce Orbih ya na shirin murde zaben ta yarda wanda ya ke so zai karbe jam’iyyar adawar.

Musa Kadiri ya jawo hankalin jiga-jigan PDP a Edo cewa idan har aka yi karfa-karfa, jam’iyyar ta na iya shan kashi a zaben gwamna na 2020.

Kadiri ya yi kira ga Jagoran PDP a Edo, Lucky Igbinedion, ya sa baki domin ganin ba a hana Kenneth Imasuangbon da Gideon Ikhine takara ba.

Kungiyar ta ce rikicin APC da kuma rashin kokarin gwamna mai-ci ya ba PDP dama a zaben bana, amma wasu na kokarin dawo da komai baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel