Malami bawan Allah: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da malaman makaranta

Malami bawan Allah: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da malaman makaranta

Kaico! Allah Sarki, wasu miyagu yan bindiga sun sace tare da garkuwa da wasu malaman makarantar firamari guda biyu a kauyen Avbiosi na karamar hukumar Owan ta yamma a jahar Edo.

Daily Trust ta ruwaito maharan sun dauke malaman makarantar ne a ranar Litinin, 13 ga watan Janairu yayin da suke tsaka da koyarwa a makarantar firamarin gwamnati na Obi Camp, malaman sun hada da Dada Okun da Esther Alabi.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje ta garkame wani babban banki saboda bashin N423m

Sai dai jim kadan bayan sace malaman, yan bindigan sun tuntubi iyalansu, inda suka nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 1 kafin su sake su, amma daga bisani suka kara kudin zuwa naira miliyan 15.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karf 10:30 na safe ne yan bindigan suka shiga makarantar, inda suka umarci malamai guda shida da su biyo su yayin da suka cigaba da harbin mai kan uwa da wabi, sai dai ana kan hanya malamai 4 suka tsere.

Bugu da kari an ci sa’a jami’an tsaro, mafarauta da matasa yan sa kai da suka bi sawunsu sun samu nasarar ceto guda daga cikin malaman, Dada Okun daga hannun miyagun, amma yana dauke da raunin sara a kansa, yayin da Malam Esther take hannunsu barayin har yanzu.

Shugaban karamar hukumar Owan ta yamma, Frank Ilaboya ya bayyana cewa suna cigaba da daukan matakan ganin sun ceto malama Esther da ranta kamar yadda mai magana da yawunsa, Hassan Otinau ya tabbatar a ranar Talata.

“Za mu cigaba da nemanta, kuma ba zamu gajiya ba har sai mun ceto ta da ran ta. Yan bindigan sun tuntubi iyalanta a daren jiya, kuma ma sun yi magana da ita, tana cikin koshin lafiya.” Inji shi.

Daga karshe ya yaba ma jami’an tsaro, matasa, mafarauta da kuma sauran jama’a da suka fita don nemo malaman da aka sace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng