Rai banza: Sama da yayan kungiyar matsafa 20 aka halaka a jahar Edo

Rai banza: Sama da yayan kungiyar matsafa 20 aka halaka a jahar Edo

Akalla mutane ashirin ne suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon wani kazamin rikici daya sake barkewa a tsakanin kungiyoyin matsafa daban daban a fadin garin Bini na jahar Edo, inji rahoton jaridar The News Express.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin wannan rikici an kashe wani ma’aikacin sa kai na hukumar gwamnatin jahar a daidai lokacin da yake bakin aikinsa a mahadar hanyar nan ta Third Junction.

KU KARANTA: An kama mai kamawa: An kama Yansandan da suka bindige wata budurwa a Abuja

Kisan wannan mutumi da yayan kungiyar matsafa suka yi ya janyo tashin hankali da fargaba a tsakanin direbobin motar haya ta Bus da yan kasuwa dake da shaguna a bakin titin, inda kowa yayi ta kansa, kafa mai naci ban baki ba.

Haka zalika a babban titin iyobosa dake kan gab da titin MM a garin Bini yan kungiyar matsafa sun kashe wani dan kungiyar hamayyarsu a ranar Lahadi 14 ga watan Oktoba, sai kuma wani ma da aka kashe a titin Sokomba.

Shi kuwa mutum ba uku ya faru ne mahadar titi ta Alohan, yayin da wasu yan bindiga dake tafe a cikin mota suka bude masa wuta a daidai lokacin da yake tafiya a kasa, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyarmu.

A ranar Asabar din data gabata ne gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ya dauki alwashin kawo karshen ayyukan yayan kungiyoyin matsafa a jahar, gwamnan ya bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa da yayi da shuwagabannin hukumomin tsaro dake jahar.

“Na gana da kwamishinan Yansandan jahar, da shugaban hukumar tsaron farin kaya, bisa karuwar ayyukan matasa yayan kungiyoyin matsafa a jahar nan, don haka zamu kashe ko nawa ne don kama masu kitsa wannan rikici, ba zamu lamunci dabi’ar nan ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel