Gwamna Ya Tube Rawanin Mai Martaba Sarki, Ya Tsige Dukkan 'Yan Majalisar Sarkin

Gwamna Ya Tube Rawanin Mai Martaba Sarki, Ya Tsige Dukkan 'Yan Majalisar Sarkin

  • Gwamnan Bayelsa Douye Diri ya janye takardar nadin sarkin masarautar Swali, Chief Wilcox Seiyefa, bisa shawarar kwamitin bincike
  • An dakatar da sarkin gargajiyar da majalisar sarakunan yankin tun a watan Mayun 2025 kan zargin hannu wajen ta'azzarar matsalar tsaro
  • Gwamnatin ta umurci tsohon sarkin da ya mika takardar shaidar amincewa da nadin sarautarsa da kuma sandar mulki da ke hannunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya tsige rawanin sarkin Swali, Mai martaba Chief Wilcox Seiyefa, daga kujerarsa ta sarautar Ebeniken.

Mataimakin gwamnan jihar, Dr Peter Akpe, ne ya sanar da matakin a madadin gwamna yayin ganawa da shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki na masarautar Swali a gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa ranar Talata.

Gwamna Douye Diri ya tube rawanin basarake a masarautar Swali, jihar Bayelsa.
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Dare ya na jagorantar taron majalisar FEC a Yenagoa. Hoto: @govdouyediri
Source: Facebook

An dakatar da sarkin tun 2025

Kara karanta wannan

'Yan kwallo sun rasu bayan hadari a Kebbi, gwamna ya ba su miliyoyin Naira

Ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin bincike da aka kafa domin duba lamarin, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

Tun a ranar 21 ga Mayun 2025, gwamnatin jihar ta dakatar da Chief Wilcox Seiyefa tare da majalisar sarakunan yankin bayan zargin cewa sun taimaka ko sun yi sakaci wajen faruwar matsalar rashin tsaro a garuruwan Swali.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa tube rawanin sarkin da aka yi ya yi daidai da sashe na shida na dokar sarautun gargajiya ta jihar, musamman wajen tabbatar da zaman lafiya, doka da kyakkyawan shugabanci.

Kwamitin bincike ya gano gazawar shugabanci

Dr Akpe ya ce kwamitin binciken ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin tare da neman shawarwarin hukumomin tsaro domin gano matakin da ya dace a dauka.

Ya ce binciken ya nuna cewa a lokacin da matsalolin tashin hankali da rashin tsaro suka faru, masarautar yankin ba ta dauki matakan da suka dace wajen shawo kan lamarin ba.

Ya ce:

“Bisa shawarar kwamitin da kuma tanadin dokar sarautar gargajiya ta jihar, gwamna ya amince da janye takardar amincewa da sandar mulki ta Chief Wilcox Job Seiyefa domin kare zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

RMAFC, NPC: Tinubu ya rantsar da sababbin kwamishinoni 8 a fadar shugaban kasa

Gwamna ya bada umarnin zabar sabon sarki a Bayelsa
Taswirar jihar Bayelsa, inda gwamna ya tsige mai martaba sarki. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Za a zabi sabon sarki cikin wata uku

Jaridar Vanguard ta rahoto mataimakin gwamnan ya ce Gwamna Diri ya umarci a fara tsarin zaben sabon sarkin Swali nan take.

Ya bayyana cewa za a kafa kwamitin zabe, kuma dole ne a kammala zaben cikin watanni uku daga ranar 30 ga Yunin 2026.

Gwamnatin jihar ta kuma umurci tsohon sarkin da ya mika takardar shaidar amincewa da nadin sarautarsa da kuma sandar mulki da ke hannunsa ga sakataren karamar hukumar Yenagoa.

A wani mataki na gaba, bisa umarnin Gwamna Douye Diri, an kafa kwamitin mutane biyar da zai jagoranci zaben sabon Ebeniken na masarautar Swali.

Diri ya tsige sarkin Ogboinbiri

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bada umarnin tsige sarkin Ogboinbiri, Okosughe Benson Eseimokumo, tare da rushe majalisar sarakuna.

Wannan mataki ya biyo bayan rikicin ranar Talata da ya yi sanadin asarar rai da kone-kone a garin na Ogboinbiri da ke ƙaramar hukumar Southern Ijaw.

Tun kafin a sanar da tsige sarkin, gwamnatin Bayelsa ta sanya dokar ta-ɓaci ta awanni 12 domin dawo da zaman lafiya a garin da ake hako man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com