INEC Ta Fara Daukar Ma'aikata domin Zaben Gwamnan Osun na 2026

INEC Ta Fara Daukar Ma'aikata domin Zaben Gwamnan Osun na 2026

  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna da za a yi a jihar Osun a watan Agustan 2026
  • INEC ta fara ɗaukar ma'aikatan wucin-gadi domin su taimaka mata gudanar da zaɓen daga 27 ga Yuni zuwa 18 ga Yulin shekarar 2026
  • Hukumar ta kafa sharudan ciki har da cewa kada masu neman aikin su kasance 'yan wata jam'iyyar siyasa ko nuna goyon baya ga 'yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Hukumar zabe ta ƙasa (INEC) ta fara ɗaukar ma'aikatan wucin-gadi domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun na 2026.

A wata sanarwa da ta fitar a makon nan, INEC ta gayyaci 'yan Najeriya da suka cancanta su nemi guraben ayyukan zaɓe daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

Shugaban INEC yana bayani
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Aikin da INEC za ta dauka

A sakon da INEC ta fitar a Facebook, hukumar ta ce za a dauki jami'an kula da shugabannin rumfunan zaɓe a Osun.

Haka zalika za ta dauki shugabannin rumfunan zaɓe, mataimakan shugabannin rumfunan zaɓe da sauransu.

INEC ta ce:

“Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na gayyatar mutanen da suka cancanta kuma suke da sha'awar yin aiki a matsayin ma'aikatan wucin-gadi domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun na 2026.”

Yaushe za a dauki ma'aikatan?

Hukumar ta ce an buɗe shafin neman aikin a ranar 27, Yuni, kuma za a rufe shi kai tsaye da tsakar dare a ranar 18, Yulin shekarar 2026

Dangane da muƙamin jami'in kula da shugabannin rumfunan zaɓe, INEC ta ce ma'aikatan gwamnatin tarayya da ke mataki na 12 zuwa 14 a ma'aikatun gwamnati da hukumomi sun cancanta.

Duk da haka za ta bayar da fifiko ga ma'aikatan jukumar NYSC, hukumar NOA, hukumar NIMC da hukumar ƙidayar jama'a ta kasa (NPC).

Kara karanta wannan

'Za a kayar da Tinubu warwas a zaben 2027,' Sanata Dickson na NDC

Ma'aikatan INEC a wajen zabe
Jami'an INEC a wajen zaben Ekiti na 2026. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa hukumar ta ce ma'aikatan INEC da ke mataki na 8 zuwa 14 waɗanda ba a ba su wasu ayyukan zaɓe ba su ma za su iya nema.

Gargadi kan shiga siyasa

Sai dai bayan sanar da wadanda za a dauka, INEC ta gargadi masu neman aikin da su guji shiga harkokin siyasa.

Ta ce:

“Mai neman aikin ba dole ne ya kasance mamba na kowace jam'iyyar siyasa ba.”

Hukumar ta ƙara da cewa:

“Mai neman aikin ba dole ne ya nuna ko bayyana goyon baya ga wani ɗan takara ko wata jam'iyyar siyasa ba.”

An kai ƙarar Tinubu wajen INEC

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar farar hula ta CFRPA ta kai korafi game da Bola Tinubu wajen hukumar zabe ta INEC.

Kungiyar ta bukaci hukumar INEC ta yi cikakken bayani game da zargin amfani da takardun bogi da ake yi wa shugaban kasar Najeriya.

CFRPA ta yi barazanar maka hukumar zabe ta kasa a gaban kotu idan ba ta fitar da cikakken bayani ba kafin babban zaben shugaban kasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng