Babbar magana: An kama wasu mutane biyu dake basaja a zuwan sune Buhari da Osinbajo

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu dake basaja a zuwan sune Buhari da Osinbajo

Wasu mutane biyu da suka hada da Amos Ehis, wani dalibi a sashen karatun harkokin kasuwanci a jami'ar Ambrose Ali da ke Ekpoma da Kelvin Ogashi, sun shiga hannun jami'an tsaro bisa zarginsu da yin sojan gona a matsayin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.

An kama su ne yayin wani atisaye na hikima da jami'an rundunar tsaron farin kaya na jihar Edo suka shirya musamman saboda masu laifin.

An kama Amos a Ubiaja da ke karamar hukumar Esan ta kudu, yayin da aka kama Kelvin mai shekaru 18 a tsohon titin Agbor da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha a jihar Edo.

Ana zargin Amos, mai shekaru 30, da bude shafin 'facebook' na bogi da sunan Osinbajo da hotonsa tare da damfarar mutane, yayin da shi kuma Kelvin ya bude shafin 'Instagram' da suna da hoton Aisha Buhari.

Da yake bajakolin masu laifin a gaban manema labarai, darektan DSS a jihar Edo, Brown Ekwoaba, wanda mataimakinsa, Mista Galadima Byange, ya wakilta, ya ce mutanen sun amsa laifinsu yayin da suke amsa tambayoyi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Katsina ta haramta sayar da baburan 'Boko Haram'

Ekwoaba ya ce, "Asuelimen ya amsa cewar ya damafari a kalla mutane biyar ta hanyar neman su aika masa kudi da katin waya domin taimaka musu don su samu rancen kudin da yawansu ya kai N100,000.

"Ogashi ya amsa cewa ya kirkiri shafi a manhajar 'instagram' da suna da hoton matar shugaban kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, domin ya damfari duk wanda ya fada tarkonsa."

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Ogashi ya ce shi tela ne kuma tunda ya bude shafin, bai taba damfarar kowa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel