APC tayi kamu a Jihar Edo bayan Godwin Esheshi ya bar Jam'iyyar PDP

APC tayi kamu a Jihar Edo bayan Godwin Esheshi ya bar Jam'iyyar PDP

Mun samu labari daga jaridar Punch ta kasar nan cewa wani fitaccen ‘dan siyasa a jihar Edo da ke Kudu maso kudancin Najeriya ya sauya sheka daga jam’iyyar hamayya zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

APC tayi kamu a Jihar Edo bayan Godwin Esheshi ya bar Jam'iyyar PDP

Wani Jigon PDP ya canza sheka a Jihar Edo ya nemi a zabi APC
Source: UGC

Godwin Esheshi, ya tattara kayan-sa ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Esheshi, tsohon jigo ne na jam’iyyar PDP a Garin Etsako da ke cikin jihar Edo. Sauyan shekan babban ‘dan siyasar yana iya kawowa PDP cikas a 2019.

Mataimakin gwamnan jihar Edo watau Philip Shaibu, shi ne ya karbi babban ‘dan siyasar da dinbin magoya bayan sa zuwa jam’iyyar APC inda aka yi masu wankan tsarki. Philip Shaibu ya nuna jin dadin sa game da wannan lamari.

KU KARANTA: 2019: PDP tayi wani taron ban mamaki a jihar Katsina

Mista Godwin Esheshi yayi jawabi a wajen taron inda ya bayyana cewa an dinke barakar da ke tsakanin sa da manyan APC don haka ya dawo. ‘Dan siyasar ya sha alwashin ganin APC tayi kokari wajen kawo cigaba a jihar Edo.

Kamar yadda mu ka samu labari, Esheshi, yayi kira ga mutanen jihar su marawa jam’iyyar APC baya 100-bisa-100 a babban zaben da za ayi a 2019. A bana dai ba za ayi zaben sabon gwamna a jihar Edo da Kogi da kuma Bayelsa ba.

Jiya kun ji cewa tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa babu mamaki a karawa IGP na 'Yan Sandan Najeriya wa’adi saboda ya murde zaben bana inda ya zargi INEC da yunkurin yi wa Shugaba Buhari aiki a zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel