Idahosa: Rikon da Oshiomhole ya ke yi wa Jam’iyya ya sa ake shirin tsige sa
Charles Idahosa, wanda ya na cikin Jagororin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Edo, ya bayyana cewa gwamnoni su na daf da tsige Adams Oshiomhole.
Mista Charles Idahosa ya kuma bayyyana dalilin da ya sa wasu Gwamnonin jihohi na jam’iyyar APC su ka dage wajen ganin bayan shugaban jam’iyyar.
A cewarsa, irin salon mulkin Adams Oshimhole a kan kujerar shugaban jam’iyya ne ya jawo masa wannan hali da ya shiga, har kuma ya ba shi shawara.
Idahosa ya na ganin cewa Oshiomhole ne ya jefa jam’iyyar a halin rigimar da ta samu kanta a dalilin irin rikon da ya ke yi wa jam’iyyar mai mulki.
Jagoran na APC ya fadawa shugaban nasa ya daina yi wa jama’a koke-koke, ya sauka daga mukamin da ya ke kai, a samu wani ya karbi kujerar.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta yi wani muhimmin taro a Garin Abuja
Mista Idahosa, a na sa ra’ayin, ya na ganin cewa zai fi kyau APC ta samu wani Bawan Allah mai madaidaicin hali ya rike ragamar jam’iyyar a Najeriya.
"Kwamred Oshiomhole ya rabu da mu da wasan kwaikwayonsa na kiran ‘Yan Najeriya su yi masa addu’a a game da rigimar da ta barkowa jam’iyyar APC."
"Yaudara ce kurum, wanda ta na cikin halinsa. Duniya ta san cewa shi ne silar rikicin da ake yi a jam’iyyar a fadin jihohi kasa da kuma sama." Inji Idahosa.
Idahosa ya kare da: “A jihohi, gwamnoni su na yunkurin tsige shi ne saboda kaushinsa, da zagon-kasa, da irin kama-karyar da ya ke yi wajen rikon jam’iyyar.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng