Zaben 2027: Peter Obi Ya Mika Bukatar da Ta Shafi Tinubu da Sauran 'Yan Takara ga INEC

Zaben 2027: Peter Obi Ya Mika Bukatar da Ta Shafi Tinubu da Sauran 'Yan Takara ga INEC

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya yi kira da babbar murya ga hukumar zabe ta INEC
  • Peter Obi ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta yi baje kolin takardun da kowane dan takara ya gabatar mata kafin zaben 2027
  • Dan takarar shugaban kasa ya nuna cewa alamun da wasu shugabanni suke nunawa, ya sanya dole a dasa ayar tambaya a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, ya mika bukatarsa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Peter Obi ya bukaci INEC da ta bayyanawa jama'a takardun shaidar karatu da 'yan takara masu neman kujeru suka mika mata.

Peter Obi ya mika bukatarsa ga INEC
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya yi wannan kiran ne yayin da yake yin magana kan tambayoyin da ke cikin fom din tsayawa takara na INEC, musamman wadanda suka shafi lafiyar kwakwalwa da sahihancin takardun karatu, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu

Wace bukata Peter Obi ya nema?

Ya bayyana cewa domin samun gaskiya a tsarin zabe, ya kamata INEC ta buga takardun karatun da dukkan masu neman takarar suka mika, jaridar TheCable ta kawo labarin.

A cewar Obi, samar da irin wadannan takardun ga jama'a zai taimaka wajen tabbatar da cewa wadanda ke neman mukaman gwamnati sun bi manyan ka'idoji na rikon amana da mutunci.

“Shin ka taba gabatar da jabu ko bogin takardar shaida ga INEC?” Har ila yau, amsar ita ce Eh ko A'a."
"Wannan yana haifar da wata muhimmiyar tambaya: Me zai hana INEC, domin tabbatar da cewa shugabanninmu sun kasance ababen koyi wajen bin dokoki da kuma karfafa gwiwar jama'a ga tsarin zabenmu, ta buga takardun karatu da kowane dan takara mai neman kujera ya mika mata?”
“Bayyanar da gaskiya tana karfafa dimokuradiyya kuma tana gina amincewar jama'a. Matsalolin Najeriya sun yi yawa da za a tsaya ana yin siyasa irin ta da can. Lokaci ya yi da za a samar da shugabanci da aka gina shi da kwarewa, hali na gari, iko, tausayawa da kuma sadaukarwa.”

Kara karanta wannan

An shigar da ƙara a jihar Kano, ana neman hana Shugaba Tinubu takara a zaben 2027

- Peter Obi

Peter Obi ya kawo hujja

Ya lura cewa sashe na E, tambaya ta 1 a fom din tsayawa takarar ya tambayi ko dan takara ya taba kasancewa wanda aka yankewa hukuncin cewa mahaukaci ne ko kuma aka bayyana shi a matsayin mutumin da ba shi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa, tare da "Eh" ko "A'a" kawai a matsayin amsoshin da za a iya bayarwa.

Peter Obi na son a bayyana takardun 'yan takara
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Obi ya ce tambayar tana tayar da damuwa game da ko shugabannin siyasa na yanzu suna nuna alamun shugabanci na mutane masu cikakkiyar lafiyar kwakwalwa.

A cewarsa, abubuwan da ke faruwa a halin yanzu a kasar da suka hada da garkuwa da mutane, rashin tsaron manyan hanyoyi, yaduwar yunwa, da kuma zargin karkatar da kudaden jama'a ta hanyar hukumomi da ayyuka masu ban al'ajabi, suna nuna cewa shugabannin siyasa sun kauce hanya kan muhimman abubuwan da suka shafi kasa.

Fadar shugaban kasa ta yi maganar Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tuna baya kan yadda Peter Obi ya lashe zabe a jihae Legas a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

2027: An miƙa bukata ga Kwankwaso da Obi bayan an fara jita jitar za su fice daga NDC

Fadar ta yi watsi da zargin cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NDC, barazana ce ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027.

Ta bayyana cewa Peter Obi ba zai sake maimaita nasarar da ya samu a Legas a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba, inda ya doke Bola Tinubu a wancan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng