Oshiomhole bai isa ya hana ni zarcewa ba – Gwamna Obaseki

Oshiomhole bai isa ya hana ni zarcewa ba – Gwamna Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya nuna karfin gwiwa a ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, cewa zai samu tikitin takarar jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC), domin zarcewa a shugabancin jihar.

A yanzu haka ana rigima tsakanin Mista Obaseki da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Ana ganin cewa mista Oshiomhole na goyon bayan wani dan takarar gwamna na APC, Osagie Ize-Iyamu a zaben 2020.

Gwamnan mai mulki ya nuna matsayarsa ne a yayinda ya karbi bakuncin shugabannin APC a karamar hukumar Eredo.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin Gwamnan, Crusoe Osagie ne ya gabatar da jawabin Gwamnan.

Gwamnan ya kuma jadadda zarginsa na cewa Oshiomhole na kokarin zama ubangida a Edo, zargin da Shugaban jam’iyyar ya karyata.

Obaseki ya bayyana cewa kokarinsa a kan mutanen Edo shine kare ra’ayinsu da kawo karshen juya jihar da wasu ke yi don kansu, wanda hakan ke barazana ya hakki da yancin damokradiyyarsu.

KU KARANTA KUMA: APC bata taba tunanin tsayar da Buhari a karo na uku ba – Gwamnan Nasarawa

Obaseki ya bukaci mambobin APC da magoya bayansu a karamar hukumar Oredo da kada su damu kansu domin shi bai damu ba tunda mutum ba Allah bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng