Miyagu sun yi gaba da wasu Malaman Makaranta a Jihar Edo

Miyagu sun yi gaba da wasu Malaman Makaranta a Jihar Edo

Wani rahoto da mu ka samu daga This Day ya bayyana cewa an samu wasu ‘Yan bindiga da su ka yi ta’adi a jihar Edo kwanan nan.

Wadannan Miyagu da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne, sun sace Malamai biyu a makarantar firamaren Avbiosi Uzebba.

‘Yan bindigan sun yi wannan barna a Kauyen na Avbiosi Uzebba da ke cikin karamar hukumar Owan ta yamma daga dawowa hutu.

Jaridar ta ce an yi wannan danyen aiki ne jiya, watau ranar farko da makarantun gwamnati da na kasuwa su ka shiga sabon zangon aiki.

Wani da abin ya auku a gabansa, ya ce ‘yan bindigan sun shigo makarantar ne da kimanin karfe 10:30 na safiyar ranar da abin ya faru.

KU KARANTA: Gwamnan Kwara ya gana da Buhari; ya mika kokon bararsa

Ya ce, “Nan su ka umarci wasu Malamai shida su bi su bayan sun yi ta sakin harbe-harbe a iska.”

“Malamai hudu daga cikin shida da aka dauka, sun kubuto, inda ‘Yan bindigan su ka yi nasarar tserewa da wasu Malamai biyu.”

“Bayan sa hannun jami’an tsaro da ‘Yan banga, an ceto Malami guda da aka sace a cikin dare inji shugaban karamar hukumar.”

Frank Ilaboya wanda shi ne shugaban karamar hukumar Owan ya bayyana cewa har yanzu Misis Esther Alabi ta na nan a tsare.

Ilaboya ta bakin Hadiminsa, ya bayyana cewa za a kubutar da wannan mata ba tare da bata lokaci ba, ya na mai tir da wannan aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel