Tinubu Ya Fadi Minista 1 da Ya Fahimci Nufin Gwamnatinsa Ga ’Yan Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yabawa ministan Abuja, Nyesom Wike kan ayyukan da ya ke gudanarwa a birnin
- Shugaban ya ce gwamnatin sa za ta tabbatar da an kashe duk kudin jama'a wurin kawo ci gaba, tare da kawo ayyukan raya ƙasa
- Wike ya gargadi 'yan kwangila da sarakunan gargajiya su guji cin hanci, yana mai cewa gwamnati ba za ta amince da haka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana game da ayyukan alheri da ministan Abuja, Nyesom Wike ke yi a babban birnin tarayya.
Tinubu ya yaba da aikin Wike ke yi yana cewa ya fahimci manufofi da hangen nesan gwamnatinsa, musamman Ajandar 'Renewed Hope'.

Source: Twitter
Tinubu, ta bakin Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da titin Gwagwalada zuwa Dafa da Yangoji mai tsawon kilomita 13, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Masoyin Tinubu ya hango matsala, ya magantu kan tsawaita wa'adin shugaban Kwastam
Tinubu ya yaba wa Nyesom Wike
Shugaban ya ce sauye-sauyen more rayuwa da Wike ya jagoranta a Abuja da ƙauyuka sun canza rayuwar al'umma, tare da ƙara amincewar jama'a ga gwamnati.
Ya ce Wike ya aiwatar da Ajandar 'Renewed Hope' ta hanyar gina ayyukan da 'yan Najeriya ke gani kuma suke amfana da su kai tsaye.
Tinubu ya ce Wike ya bi umarninsa na faɗaɗa ci gaba zuwa ƙananan hukumomi, ta hanyar gina ingantattun hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Ya ce yadda ministan ke sa ido kan ayyuka, dagewa kan inganci da kammala su akan lokaci ya zama abin koyi a aikin gwamnati.
A cewarsa, gwamnati ba za ta bari ci gaba ya tsaya a tsakiyar Abuja kawai ba, domin dole ne ci gaba ya kai ga kowane ɗan Najeriya, ciki har da mazauna karkara.

Source: Facebook
Gargadin Tinubu, Wike kan yan kwangila
Shugaban ya bayyana titin a matsayin muhimmiyar hanyar bunƙasa tattalin arziki, noma, kasuwanci, ilimi da kiwon lafiya a Ƙaramar Hukumar Kwali.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
Ya kuma jaddada cewa zamanin fara ayyuka ba tare da kammala su ba ya ƙare, domin gwamnati za ta tabbatar da an kammala kuma an kula da dukkan ayyuka.
Tinubu ya yabawa Wike, manyan sakatarori da jami'an hukumar saboda haɗin kai wajen hanzarta aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
A nasa jawabin, Nyesom Wike ya gargadi sarakunan gargajiya da 'yan kwangila da su guji neman cin hanci ko anfani na kansu daga ayyukan gwamnati.
Ya ce a wasu wurare, sarakuna kan fara tambayar abin da za su samu daga ɗan kwangila maimakon tabbatar da an kammala aikin yadda ya kamata, cewar Daily Post.
'Ba mu da wanda ya fi Tinubu' - Wike
Mun ba ku labarin cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da sake zaben Bola Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara.
Wike ya ce Rivers ba ta da wani zaɓi illa ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 domin samar da ci gaba.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta bai wa Rivers muƙamai da ayyukan ci gaba fiye da gwamnatocin baya, yana mai kira ga jama'a su yaba.
Asali: Legit.ng