Wata Malama da ta yi fice a koyarwa ta samu kyautan kayataccen gida a Edo
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya mika kyautar wani kayataccen gida mai dakuna biyu ga wata Malamar makaranta da aka yi ittifaki babu kamarta wajen iya koyarwa tare da bada gudunmuwa ga ilimi a jahar Edo gabaki daya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya mika makullan gidan ne ga Malama Noragbon Osaru a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu yayin daya kai ziyara jahar Edo inda ya kaddamar da sabbin rukunin gidaje guda 100 da gwamnatin jahar ta gina.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun karkashe yan ta’adda, sun kama kwamandansu a Borno
A jawabinsa, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya danganta nasarar da matar ta samu ga kokarinta a yayin koyar da dalibai “Ina miki makullan gidannan ne sakamakon sadaukarwa da jajircewa da kike nunawa a bakin aiki” Inji shi.
Yayin da gwamnan jahar Edo, Mista Godwin Obaseki yake nasa jawabin, ya tuna ma Osinbajo cewa rukunin gidajen da yake gani sune wadanda ya sanya tubalin fara gininsu a kimanin shekaru biyu da suka gabata.
“Wadannan sune rukunin gidajen Emotan daka sanya tubalin fara ginasu a shekaru biyu da suka shude, a yanzu mun kammala guda dari daga cikinsu, a matsayinmu na gwamnati mun sayi guda 10, sa’annan mun sayar ma jama’a guda 50. Sa’annan mun sadaukar da gida daya kyauta ga Malamar da tafi kwarewa wajen iya koyarwa” Inji shi.
A watan yunin shekarar 2017 ne mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya kaddamar da fara ginin gidaje dubu daya da dari bakwai da ashirin da bakwai a unguwar Egba, cikin karamar hukumar Ikpoba Okha ta jahar Edo.
A wani labarin kuma, Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da tsarin ciyar da daliban makarantun Firamari da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kirkira.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng