Man fetur: Kusan Dala Biliyan 1.35 mu ka rasa a 2019 Q1 - Obaseki

Man fetur: Kusan Dala Biliyan 1.35 mu ka rasa a 2019 Q1 - Obaseki

Mai girma gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya koka a game da yawan satar danyan man da ake yi wa Najeriya a yankin Neja-Delta. Wannan ya na jawowa kasar asara duk shekara.

Godwin Obaseki ya ce a sanadiyyar wannan satar mai, Najeriya ta rasa sama da ganguna miliyan 22 na danyen mai. Najeriya ta gamu da wannan asara ne a cikin watanni hudun farkon bana.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da shugabannin kungiyar PANDEF na mutanen Neja-Delta su ka kawo masa ziyara a gidan gwamnati da ke babban birin jihar na Benin Ranar Lahadi.

Mai girma gwamnan ya kiyasta asarar gangunan da Najeriya ta yi a matsayin Dala biliyan 1.35. A kudin Najeriya wadannan kudi sun haura Naira biliyan 400, watau kusan rabin Tiriliyan na Naira.

“Ganin cewa na shugabanci kwamitin satar danyan mai a majalisar NEC, abin tada hankalin shi ne irin ta’adin Tsageru da ke yankinmu. Ba a san inda gangunan mai miliyan 22 su ka shige ba.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kasa ya tsare a kan binciken ke-ke-da-ke-ke a Neja Delta

“A cikin rabin farkon shekarar nan, babu wanda zai iya cewa ga inda gangunan su ka shige. Wannan ya nufin Biliyan 1.35 sun shiga hannun wasu mutane da ba gwamnati bane a yankin.”

Gwamnan na APC ya kuma yi tir da ikirarin da ake yi na cewa an kashe makudan kudi a yankin na Neja-Delta a shekarun baya. Yanzu dai babu wata alama da ke nuna an amfana da kudin.

A game da wannan barna, Obaseki ya kara da cewa: “Akwai bukatar ayi amfani da dukiyar kasar wajen habaka tattalin arziki domin hana a yi wa mutanen Neja-Delta cogen dukiyar kasar su.

Tsohon Sufetan 'Yan Sandan Najeriya, Solomon Arase, shi ne shugaban PANDEF a jihar Edo inda ya kawowa gwamnan ziyara domin yi masa bayani a game da wasu batutuwa da ke damun jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng