NDC: Yaron Atiku Ya Nemi ADC, PDP da Sauran Jam’iyyu Su Taya Obi da Kwankwaso Fada
- Ganin kotu ta soke rajistar NDC, an samu masu taya babbar jam’iyyar hamayyar takaicin mummunan abin da ya faru da ita
- Shehu Atiku Abubakar ya yi kira ga sauran ‘yan jam’iyyun ADC da PDP su tashi tsaye domin a taya NDC yakar soke rajistar
- Idan Shehu ya samu yadda yake so, mutane za su fita kan tituna su yi zanga-zanga domin yana ganin da hannun gwamnatin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukuncin kotun tarayya mai zama a garin Lokoja, jihar Kogi wajen dakatar da rajistar jam’iyyar hamayya ta NDC ya jawo maganganu.
Wasu ‘yan siyasa musamman ‘yan adawa a Najeriya sun soki wannan hukuncin, suna masu zargin cewa akwai hannun gwamnatin APC a hukuncin.

Source: Facebook
Shehu Atiku bai goyon bayan soke rajistar NDC
Shehu Atiku Abubakar ya yi tir da hukuncin babban kotun tarayya, ya kuma bayyana fushinsa a gaban duniya a dandalin sada zumuntansa na X.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: An farmaki 'dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a wurin jana'iza
Malam Shehu Atiku Abubakar wanda ‘da ne ga ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, ya ajiye sabanin siyasarsu da ‘yan bangaren NDC.
Peter Obi wanda yake neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NDC ya kasance yana da kusanci da gidan Atiku Abubakar tun 2018 kafin ya canza gida.
NDC: Shehu Atiku ya ce an yi sakarci
A rubutun da ya yi safiyar Litinin, Shehu Atiku ya kira abin da ya faru da jam’iyyar NDC a kotu da sakarci kuma ya bukaci a tashi tsaye a yaki hukuncin.
Kiran na shi ya hada da manyan jam’iyyun adawa na ADC, NDC da kuma tsagin Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar PDP da Atiku ya bari a bara.
Idan aka hau tituna ana zanga-zanga, Shehu Atiku yana ganin ‘yan adawa za su aika wa gwamnatin tarayya sako cewa ba za su yarda da hukuncin ba.
A tunaninsa, tsit da ‘yan adawa suka yi ne zai jawo hakan ya cigaba da faruwa a damukaradiyya.
“Dole ADC, NDC, PDP (bangaren Turaki) da sauran ‘ya ‘yan jam’iyyun hamayya, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran ‘yan Najeriya su hau kan tituna domin nun awa gwamnatin tarayya ta APC cewa za mu iya yin komai domin kare damukaradiyyarmu.

Kara karanta wannan
2027: An miƙa bukata ga Kwankwaso da Obi bayan an fara jita jitar za su fice daga NDC
Gwamnati ta latsa tana son jarraba shirun mu ne da wannan sakarcin na lamarin NDC. Dole mu dauki mataki!"

Source: Getty Images
Yaron Atiku ya jawo muhawara a dandalin X
Wasu sun rungumi shawarar shi har aka ji wani mai suna Naija Senator a X yana cewa idan aka tafi haka, sai an ga bayan sauran jam’iyyun.
"Za su zo kan kowa. Mun dauka cewa wannan ya shafi ADC ko NDC ne."
- Naija Senator.
Shi kuwa wani Alanrewaju Abimbola cewa ya yi kyau a yi wa shugabannin Arewa zanga-zanga ne a kan matsalar tsaro, talauci da almajirai a yankin.
Da yake ba shi amsa, wani bawan Allah kuwa cewa ya yi lamarin zai zo kan kowa, kuma ya zargi jam’iyyar ADC da yin murnar abin da ke faruwa da NDC.
“Ai ADC tana ta murna, saura jam’iyyar ADC.”
Takarar Obi/Kwankwaso tana nan - Obidient
An ji labari kungiyar Obidient ta aika sako ga magoya bayanta dangane da takarar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso bayan hukuncin da kotu ta yanke kan rajistar NDC.
Shugaban kungiyar na kasa, Dr. Yunusa Tanko, ya bayyana cewa Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso za su kasance a zaben 2027 duk da matsalar kotu.
A wani jawabi da ya fitar a farkon makon nan, Yunusa Tanko ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta girmama 'yancin bangaren shari'a na kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
