Cin amana ruwa ruwa: Karamin yaro dan shekara 16 aikata ma Uwardakinsa danyen aiki

Cin amana ruwa ruwa: Karamin yaro dan shekara 16 aikata ma Uwardakinsa danyen aiki

Rundunar Yansandan jahar Edo ta sanar da cafke wani karamin yaro dan shekara goma sha shida mai suna Zakaria Chiahemba akan zarginsa da halaka uwardakinsa mai suna Rejoice Odogwu mai shekaru hamsin da uku a rayuwa.

Majiyar Legit.com ta ruwaito yaron ya kashe uwardakin tasa ce da gidanta dake gida mai lamba 25 akan titin Osazuwa dake unguwar Oluku cikin karamar hukumar Ovia ta Arewa ta jahar Edo, inda yayi amfani da adda wajen kasheta, sa’annan ya kwashe kudi, wayoyi da zinari.

KU KARANTA: Bahallatsar naira biliyan 9: Gwamna El-Rufai ya maka jami’ar ABU da KadPoly gaban kotu

Kwamishinan Yansandan jahar Edo, Babatunde Kokumo ne ya bayyana haka ga manema labaru yayin da yake gabatar da yaron a babban ofishin Yansandan jahar dake garin Bini, inda yace Zakaria yayi amfani ne da adda, gatari da icce wajen kashe matar.

“Bayan ya kashe sai ya tattara wayoyinta, sarkokin zinari da kuma wasu kudadenta yayi awon gaba dasu ya bar gari, tun daga wancan lokaci muka shiga farautarsa, bamu kamashi ba har sai ranar Juma’a 23 ga watan Nuwamba inda dubunsa ta cika a jahar Taraba.” Inji Kwamishina Babatunde.

Sai dai dayake zantawa da yan jaridu, Zakaria ya musanta zargin da ake yi masa na kashe Madam Rejoice, inda yace wasu kwastomominsu ne suka far ma gidansu a ranar suka shiga dukar matar har ta mutu saboda wai a sace wayarsu a shagonta, kuma bata wani kokarin ganin an gano wayar.

Daga karshe kwamishinan ya bayyana cewa zasu gurfanar da yaron gaban kotun da zarar sun kammala gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, wani dan tatsitsin yaro dan shekara 16 mai suna Muhammadu ya halaka wata yarinya mai suna Fatima Isah a kauyensu dake Evutagi cikin karamar hukumar Katcha na jahar Neja saboda wai bata sonsa, ba ta yarda ta aureshi ba.

Muhammadu ya bayyana cewa kishi ne ya kwasheshi har ta kai ga ya halaka Fatima bayan taki amincewa da shi, inda ta nuna karara tafi son yayansa, don haka ita kam ba tsararsa bace.

Bugu da kari maganan aure tsakanin Fatima Isah da yayan Muhammadu ya kankama, tun bayan da mahainta Isah Evutagi ya bayyana amincewarsa ga yayan Muhammadu daya auri diyarsa Fatima.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel