Yajin aikin ASUU
Kungiyar ASUU ta fadi abin da zai hana Malaman jami'a komawa aiki har yau, kungiyar ta ce ta na kokarin ta yi maza-maza ta gama magana da gwamnati duk runtsi.
Ministan ilmi, Adamu Adamu, ya ce alkawarin da aka yi wa ASUU a baya ya jawo matsala. A lokacin PDP ne gwamnatin tarayya ta yi wa Jami’o’i alkawarin N1.3tr.
A yanzu an dauki wata bakwai ana yajin-aiki a Jami’o’i har yau ba a samu mafita ba. Minista ya caccaki Malamai, Kungiyar ASUU ta karyata Gwamnatin tarayya.
Malaman Jami’a sun yi magana game da yajin-aikinsu, sun zargi Gwamnati da kawo cikas, su ka ce rashin amince wa da UTAS ne ya tsaida maganar koma wa karatu.
ASUU ta ce ta na fafutuka ne domin a gyara Jami’o’in Gwamnati. Malaman Jami'a sun sha alwashin jan yajin-aiki har sai an biya su duk albashinsu da su ke bi.
Za ku ji yadda zaman karshe na Malaman Jami’a da Gwamnati ta kaya. An yarda za a kammala biyan duk wasu kudin ASUU ke bi daga Mayun 2021 zuwa Fubrairun 2022.
Shugabannin ASUU da gwamnatin tarayya sun tattauna akan yajin aikin malaman jami'o'i, kuma daga yadda al'amara suke tafiya, malamai na duk shirye-shiryn komawa.
Mun ji cewa Kungiyoyin National Professional Group da Northern Nigerian Youths Frontiers sun bukaci gwamnonin Zamfara da Borno su sa baki domin a bude Jami’o’i.
Gwamnatin tarayyar Najeriya yayin taron tattaunawa da ta ke yi da kungiyar malaman jami'o'i na kasa, ASUU ta yi amince za ta biya malaman kudi N30bn na allawus.
Yajin aikin ASUU
Samu kari