FG ta amince za ta biya 'yan kungiyar ASUU kudin allawus N30bn

FG ta amince za ta biya 'yan kungiyar ASUU kudin allawus N30bn

- Gwamnatin tarayya ta amince za ta biya kungiyar ASUU kudi Naira biliyan 30 na allawus din malaman jami'o'in

- Gwamnatin ta ce za ta fara biyan kudin daga watan Mayun shekarar 2021 zuwa Fabrairun shekarar 2022

- Har ila yau, gwamnatin ta amince za ta kashe Naira biliyan 20 a bangaren farfado da ilimin jami'o'i a fadin kasar

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar aure da ɗan ta a Katsina

Yajin aikin ASUU: FG ta amince za ta biya N30bn allawus din malamai
Chris Ngige: Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayyar Najeriya, FG, ta amince za ta biya Naira biliyan 30 kudin allawus na malaman da ke koyarwa a jami'o'in kasar.

Sai dai ba lokaci guda gwamnatin za ta biya kudin ba inda ta ce za ta biya daga watan Mayun 2021 zuwa Fabrairun 2022.

The Punch ta kuma ruwaito cewa gwamnatin tarayyar ta yi alkawarin kashe Naira biliyan 20 domin farfado da fanin ilimi a kasar yayin tattaunawar da suka yi don ganin an kawo karshen yakin aiki da ASUU ta yi watanni bakwai tana yi.

Wadannan na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma wurin tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'i'i wato ASUU a ranar Alhamis.

KU KARANTA: An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

Tunda farko kafin ya shiga taron, Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ya ce rufe makarantun da ASUU ta yi ne ya ingiza dalibai shiga zanga-zangar #EndSARS da matasan suka kwashe kwanaki suna yi.

Ngige da karamin ministan sa Festus Keyamo (SAN) ne suka jagoranci tawagar gwamnati yayin da Farfesa Biodun Ogunyemi, shugaban kungiyar ASUU ya jagoranci malaman jami'an.

A wani labarin daban, Gwamnatin ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel