Ana Jiran Martanin Kim Jong Un bayan Trump Ya Fadi Wata Magana a Kansa
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya amsa buƙatarsa ta tattaunawa da shi a wata magana da suka yi
- Trump ya bayyana cewa musayar saƙonnin da aka yi tsakaninsa da Kim ta haifar da “kyakkyawan sakamako”, duk da cewa bai yi ƙarin bayani ba
- Furucin Trump ya zo ne kwana guda bayan ya umarci Pentagon da rage yawan atisayen soji da Amurka ke gudanarwa tare da Koriya ta Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya amsa buƙatarsa ta tattaunawa, bayan da ya nemi sake farfaɗo da hulɗar kai tsaye tsakaninsu.
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da manema labarai suka tambaye shi a Fadar White House dalilin da ya sa Kim bai amsa buƙatarsa ta tattaunawa ba.

Source: Getty Images
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa shugaba Donald Trump ya mayar da martani da cewa: “Ta yaya kuka san bai amsa ba?”
Lokacin da aka sake tambayarsa, Trump ya ce:
“Eh, ya amsa.”
Shugaban na Amurka ya ƙara bayyana musayar saƙonnin da cewa tana da “kyakkyawan sakamako”, sai dai bai bayyana ƙarin bayani kan abin da suka tattauna ba.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani martani kai tsaye daga gwamnatin Koriya ta Arewa.
Trump ya rage soji a Koriya
Furucin Trump ya zo ne kwana guda bayan ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, da ta rage yawan atisayen sojin da Amurka ke gudanarwa tare da Koriya ta Kudu.
Trump ya ce a atisayen na shekara-shekara, bayan suna kashe kuɗi masu yaws, suna aika saƙon da bai dace ba kuma mai nuna ƙiyayya ga Koriya ta Arewa.
Rahoton Reuters nuna cewa ya kuma danganta matakin da matakin Koriya ta Kudu na ƙin taimakawa Amurka da Isra’ila a yaƙin da ake yi da Iran.
Trump ya soki Koriya ta Kudu
Trump ya sake sukar Koriya ta Kudu kan matsayinta game da yaƙin Iran yayin da yake magana da manema labarai a Fadar White House.
Ya ce Amurka tana da sojoji kusan 39,000 a Koriya ta Kudu domin kare ƙasar daga Kim Jong Un, amma Seoul ba ta son taimaka wa Amurka a abin da ya bayyana a matsayin “aikin soji mai sauƙi” a Iran.
Trump ya kuma sake tambayar ko ya kamata Amurka ta ci gaba da kare Koriya ta Kudu da sauran ƙawayenta na NATO waɗanda ba sa son taimakawa a yaƙin Iran.

Source: Getty Images
A nasa ɓangaren, jami’an Koriya ta Kudu sun ce atisayen sojin ya fara kamar yadda aka tsara, tare da bayyana fatan cewa kyakkyawar alaƙar Trump da Kim za ta taimaka wajen dawo da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.
Fadar Shugaban Ƙasar Koriya ta Kudu ta ce atisayen ba ya nuna wata niyya ta kai hari kan Koriya ta Arewa ko ƙara tashin hankali a yankin.
Batun sakin Ba'amurke a Nijar
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Ba’amurke Kevin Rideout, wanda aka yi garkuwa da shi a Nijar, ya sake haɗuwa da iyalansa bayan shafe watanni a tsare.
Rideout, mai shekaru 50, matukin jirgin sama ne da ke aiki da wata ƙungiyar mishan ta Kirista. An sako shi daga hannun masu garkuwa da shi a Nijar, tare da taimakon kwamandan sojin gabashin Libya, Khalifa Haftar, a cewar wasu majiyoyi.
Rahotanni sun ce sakin nasa ya zo ne kusan watanni uku bayan da sojojin Amurka suka kashe Abu Bakr al-Mainuki, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar ISIS a duniya.
Asali: Legit.ng


