ASUU: Muddin za a cigaba da rike mana albashi, yajin-aiki ba zai kare ba
- Shugaban ASUU ya ce su na fafutuka ne domin a gyara Jami’o’in Gwamnati
- Biodun Ogunyemi ya ce wasu malamai sun shafe watanni rututu babu albashi
- Farfesan ya ke cewa muddin ba a biya su kudinsu ba, babu batun a koma aiki
A tashin farko, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana abubuwan da su ke bukata wajen gwamnati.
“Gyara jami’o’i, sake tattauna yarjejeniyar 2009, batun alawus din EAA, samun karuwar jami’o’i da bada damar malami ya rika kai ziyara wata jami’ar.”
KU KARANTA: Malaman UNIMAID sun yi wata da watanni babu albashi - ASUU
A game da lamarin IPPIS, shugaban kungiyar malaman jami’ar ya ce sun kawo manhajar UTAS kuma sun gabatar da ita gaban ministoci da ‘yan majalisa.
Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce tun da har an kai ga wannan, babu dalilin da zai sa gwamnati ta cigaba da rike masu albashi, wasu na tsawon watanni tara.
“Mu na jin cewa gwamnati ta yi wannan ne domin ta rincabar da maganar, sannan duk da ta yi alkawarin cika bukatunmu, ba mu fara ganin an fara aiki ba.”
“’Yan ASUU suna da ‘ya ‘ya a jami’o’in gwamnati, amma mu na so wadannan yaran su san cewa saboda su mu ke wannan fada, mu na so su samu ilmi mai kyau.”
KU KARANTA: Za mu duba manhajar UTAS da ASUU su ka kawo - Gwamnati
Shugaban ASUU ya ce kokarin da su ke yi shi ne ganin an samu wuraren karatu, dakunan bincike da dakunan barci kamar yadda ake da su a shekarun 1970-80.
Game da yawan zuwa yaji, Farfesan ya ce: “Babu wani lokaci da za mu tafi yaji ba tare da mun duba wasu hanyoyi ba; rubuta wasika, lallashi da kamun kafa.”
Kwanakin baya Shugaban ASUU ya fito ya yi jawabi, ya ce sai inda karfinsu ya kare a wajen kare makarantun gwamnati bayan an bukaci su yi rajista da IPPIS.
Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce Kungiyar ASUU ba za ta yarda ta shiga tsarin IPPIS ba. Malaman jami’ar sun kuma ce gwamnati ba ta isa ta hana su albashinsu ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng