Saurayi Ya Yi Jima'i da Budurwa, Ya Fille Mata Wuya Ta Mutu Ya Sha Jinin Ta a otel
- Wani matashi mai shekaru 27, Ali Haruna, ya amsa cewa ya kashe wata mata mai suna Aisha tare da fille mata kai a cikin wani otal da ke ƙaramar hukumar Girei ta Jihar Adamawa
- An kama Haruna, wanda ya fito daga Kaleri a Maiduguri, Jihar Borno, a ranar Juma’ar da ta gabata bisa zargin aikata kisan gillar a wani otal da ke garin Girei, da ke wajen Yola
- Yayin amsa tambayoyi, ya bayyana cewa ya haɗu da marigayiyar ne a karon farko a otal ɗin, inda suka sha tabar wiwi tare kuma suka yi jima’i kafin lamarin ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa – Wani matashi mai shekaru 27, Ali Haruna, ya amsa zargin kashe wata budurwa mai suna Aisha tare da fille mata kai a wani otal da ke ƙaramar hukumar Girei ta Jihar Adamawa.
Haruna, wanda ɗan asalin Kaleri ne da ke Maiduguri a Jihar Borno, an kama shi a ranar Juma’a da ta gabata bayan zargin kisan matar a wani otal da ke Girei, kusa da Yola.

Source: Original
Daily Trust ta wallafa cewa matashin wanda a yanzu yake zaune a garin Digno da ke ƙaramar hukumar Fufore, ya yi wannan ikirari ne yayin da yake magana a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa da ke Yola.
Yadda aka kashe budurwar
Haruna ya ce ya fara haɗuwa da matar ne a otal ɗin, inda suka sha tabar wiwi tare sannan suka yi jima’i kafin lamarin ya rikide zuwa kisan kai.
Ya amsa cewa ya kashe matar, sannan ya yi wani ikirari mai tayar da hankali cewa daga baya ya sha jininta.
Wannan ikirari ya ƙara tayar da hankula kan ainihin abin da ya faru da matar da kuma abubuwan da suka kai ga kisan nata.
‘Yan sanda sun kama shi
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da kama wanda ake zargi da kashe budurar.
Sahara Reporters ta wallafa cewa Nguroje ya ce Haruna yana hannun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Source: Twitter
Suleiman Ngurore ya bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma tabbatar da cewa za ta gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru tare da tabbatar da cewa wanda ake zargin ya fuskanci hukunci bisa doka idan aka tabbatar da laifinsa.
Hare-haren Lakurawa a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa sama da mayakan Lakurawa 300 da ake zargi sun mamaye garin Kebbe da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce mayakan, wadanda ke kan babura kuma dauke da muggan makamai, sun yi arangama da jami’an tsaro tare da kai hare-hare kan shaguna, wani asibiti da motoci.
Wani masani kan harkokin tsaro a Sokoto, Bashar Altine, ya ce mayakan sun shiga garin da misalin ƙarfe 10:00 na safe, lamarin da ya sa sojojin da ke sansanin soja a wajen garin suka buɗe musu wuta..
Asali: Legit.ng

