Shugaban ASUU ya musanya ikirarin cewa Malamai 57, 000 su na kan IPPIS

Shugaban ASUU ya musanya ikirarin cewa Malamai 57, 000 su na kan IPPIS

- Ministan ilmi ya ce kusan 80% na kungiyar ASUU sun yi rajista a IPPIS

- Kungiyar ASUU ta karyata Ministan kasar, ta ce sam ba gaskiya ba ne

- An yi wata bakwai ana yajin-aiki a Jami’o’i, ba a samu wata mafita ba

Jaridar Punch ta ce a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, 2020, gwamnatin tarayya ta soki kungiyar ASUU, ta ce akwai abin rikitar wa game da bukatunta.

Karamin ministan ilmi na kasa, Emeka Nwajiuba, ya bayyana haka a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida game da abin da ya shafi tsarin IPPIS da aka kawo.

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a da ke yajin-aiki tun watan Maris ta maida martani, ta ce Ministan ya na kokarin hada ‘yan Najeriya fada ne da malamai.

KU KARANTA: ASUU ta maidawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari martani

A watan Oktoba an yi tunanin za a shawo kan dogon yajin-aikin da ake yi inda ASUU ta bijire wa IPPIS, sannan ta zargi gwamnatin tarayya da saba alkawuranta.

“Mun rasa gane wasu batutuwa ne kungiyar ASUU ta ke so a zauna a kai, da wadanda ba ta bukatar a tattaunasu.” Emeka Nwajiuba ya fada, ya na caccakar ASUU.

Honarabul Nwajiuba ya ce ba za su amince da manhajar UTAS da ASUU ta kawo ba, har sai an yi gwaji, Ministan ya ce idan aka yi haka, babu amfanin kawo IPPIS.

Ministan ya kuma ce: “Cikin malamai 71, 000, an samu 57, 000 da tuni su na kan IPPIS. Ban ga dalilin yajin-aikin ba, Ban ga dalilin da za su ce ba su son IPPIS ba.”

KU KARANTA: Gwamnati ta yi maganar yiwuwar karbar manhajar UTAS a madadin IPPIS

Shugaban ASUU ya musanya ikirarin cewa Malamai 57, 000 su na kan IPPIS
Ministoci da Shugabannin ASUU Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Shugaban ASUU, ya karyata Ministan, ya ce: “A bakin saninmu, wannan adadi ba gaskiya ba ne. Mun zauna da gwamnati, an kuma ba mu wasu alkaluma dabam.”

“A bincikenmu, mun gano ba su yi wa daya bisa hudu na malaman jami’a rajista a IPPIS ba. Idan su na tunanin haka, to wasa su ke yi, ya nuna mana su.” Inji Ogunyemi.

A baya ASUU ta yi magana, ta ce ta na fafutuka ne domin a gyara Jami’o’in Gwamnati. Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya ce a dalilin haka aka daina biyan malamai.

Farfesa Ogunyemi ya ke cewa sun shafe watanni rututu ba su samun albashi kuma muddin gwamnatin tarayya ba ta ta biya su kudinsu ba, babu batun su koma aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel