Ga lokacin da ASUU za ta janye yajin aiki - Kungiyar da FG sun cimma matsaya

Ga lokacin da ASUU za ta janye yajin aiki - Kungiyar da FG sun cimma matsaya

- Alamu sun nuna cewa, nan ba da jimawa ba yajin aikin da ASUU suka dade suna yi ya kusa zuwa karshe

- A ranar Alhamis,15 ga watan Oktoba ne aka yi wata doguwar tattaunawa da shugabannin kungiyar da gwamnatin tarayya

- Kamar yadda al'amarin ke tafiya, malaman makaranta na kokarin ganin sun koma makarantu ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba

Shugabannin ASUU da gwamnatin tarayya sun tattauna akan yajin aikin malaman jami'o'i, kuma daga yadda al'amura suke tafiya, malamai na yin shirye-shiryen komawa makarantu.

Jaridar Legit.ng ta tunatar da taron daidaitawa da ASUU tayi da gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, inda gwamnati ta amince da biyan Naira Biliyan 30 don biyan ASUU.

Kamar yadda ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige yace, za'a biya kudin ne tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Janairun 2022.

KU KARANTA: EndSARS: Kuna da hakkin yin zanga-zanga - Buhari ya sanar da matasa

ASUU ta amince da wannan yarjejeniyar, daga wata majiya mai karfi, ASUU na kokarin yadda makamai don shirye-shiryen komawa makarantu a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba, bayan jin shirin da ma'aikatun Ilimi da na kudi suna yunkurin sakin kudin.

Ga lokacin da ASUU za ta janye yajin aiki - Kungiyar da FG sun cimma matsaya
Ga lokacin da ASUU za ta janye yajin aiki - Kungiyar da FG sun cimma matsaya. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance

A wani labari na daban, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fatattaki shugaban hukumar hakkin mallaka, Tony Jaja, jaridar Punch ta wallafa.

An samu wannan labarin ne a wata takarda da kakakin ministan shari'a na kasa, Dr. Umar Gwanda, ya gabatar a ranar Litinin.

Babban sakataren ma'aikatar shari'a ta kasa, Dayo Apata (SAN), yasa hannu a takardar ranar 15 ga watan Oktoban 2020.

Dare ya sanar da manema labaran cikin gidan gwamnati, cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki masu zanga-zangar da su dakata na wani lokaci don ba wa gwamnati dama, don yanzu haka an fara magance matsalar su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel