Gwamnati ta hana zamanta da Kungiyar ASUU ya tafi salin-alin inji Ogunyemi

Gwamnati ta hana zamanta da Kungiyar ASUU ya tafi salin-alin inji Ogunyemi

- ASUU ta ce Gwamnatin Tarayya ba ta da niyyar kawo karshen yajin-aikinta

- Malaman Jami’ar sun zargi Gwamnati da hana tattaunawar tafiya da kyau

- Shugaban ASUU ya ce kin amince wa da manhajar UTAS ya tsaida magana

Punch ta rahoto cewa kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta zargi gwamnatin tarayya ta neman fusata yunkurin da ake yi na kawo karshen yajin-aiki.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana haka a lokacin da aka yi hira da shi a shirin Politics Today a gidan talabijin na Channels.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ki daukar matakan da su ka dace na ganin an janye dogon yajin aikin da ake yi a jami’o’i.

KU KARANTA: Bukatu 6 da ASUU ta kai gaban teburin Shugaba Buhari

Biodun Ogunyemi ya ce jinkirin da gwamnati ta ke yi wajen amince wa da manhajar UTAS da malamai su ka kirkiro, shi ne babban abin da ya ke jawo cikas.

Ya ce: “Har yanzu ana yajin-aiki a dalilin kin gwamnati na daukar matakan da su ka dace. Mun ba su makonni biyu su duba bukatu biyar da mu ka gabatar.”

“Mun zauna da gwamnati, amma ba ta da niyyar kawo karshen lamarin. Sun samu tsawon shekara su duba lamarin. Amma sun yi mana tayin abin da ba mu dauka ba.”

Farfesan ya ce sun gabatar da UTAS gaban Ministan ilmi, shugabannin majalisar dattawa da ofishin babban akawun gwamnati, kuma sun yi na’am da manhajar.

KU KARANTA: Ko UTAS, ko rijiya, ASUU ta ce Allan-barin ba za ta shiga IPPIS ba

Gwamnati ta hana zamanta da Kungiyar ASUU ya tafi salin-alin inji Ogunyemi
ASUU a taro Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

“Mun kusa samu a amince da UTAS, sai kuma gwamnati ta ke cewa mu fara shiga IPPIS, daga nan sai a koma UTAS. Babu hankali a wannan!” inji Farfesan.

“Sun ce za a biyamu idan mun koma IPPIS.” ASUU ta ce malaman jami’a ba za su yarda da hakan ba.

A watan jiya Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa Ministocin kudi, ilimi, kwadago da ofishin babban akawun gwwamnati za su zauna da ASUU.

Ma’aikatan Jami’an su na kuka a kan tsarin IPPIS, sun kuma ce an hana su wasu alawus da kudin gyara jami'o'i. Har yanzu ba a iya shawo kan bakin zaren ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng