SDP: 'Yadda Nasarar Osun Ta Fito da Gazawar APC a Najeriya'
- Jam'iyyar SDP ta ce sakamakon zaben gwamnan Osun ya rusa tunanin cewa APC mai mulkin Najeriya ba za a iya kayar da ita a siyasa ba
- Jam’iyyar ta ce nasarar Adeleke ta nuna cewa masu kada kuri’a za su iya kayar da gwamnati mai ci, tsarin siyasa da kuma tasirin kudi
- Shugaban SDP, Farfesa Sadiq Gombe, ya gargadi jam’iyyar APC cewa za a iya kayar da ita a zaben 2027 mai zuwa ba tare da gargada ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar SDP ta ce sakamakon zaben gwamnan Jihar Osun ya rusa tunanin da ake yi cewa jam’iyyar APC ba za a iya kayar da ita a fagen siyasa ba.
Jam’iyyar ta ce zaben ya nuna cewa masu kada kuri’a da suka kuduri aniyar zabar dan takarar da suke so za su iya shawo kan karfin gwamnati mai ci, tsarin siyasa da kuma tasirin kudade.

Source: Facebook
Arise News ta kawo labarin cewa shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Farfesa Sadiq Gombe, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce sakamakon zaben Osun ya aike da sako mai karfi ga jam’iyyar da ke mulki gabanin babban zaben 2027.
SDP ta yi magana kan APC
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sadiq Gombe ya ce zaben ya kuma kunshi darussa ga jam’iyyun adawa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), jami’an tsaro da kuma masu kada kuri’a.
Ya ce babban darasin da aka koya shi ne cewa bambancin da ke tsakanin manyan jam’iyyu da kananan jam’iyyu ba ya da muhimmanci sosai idan masu kada kuri’a sun riga sun yanke shawarar dan takarar da suke son zaba.
A kalamansa:
“Mutanen Osun sun koyar da ’yan Najeriya babban darasi."
Ya kara da cewa nasarar zabe ta fi dogara ne da amincewar masu kada kuri’a, ba wai girman jam’iyya, tsarinta ko karfin kudinta ba.

Kara karanta wannan
Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027
Ya kamata APC ta hankalta - SDP
Ya ce sakamakon zaben ya kamata ya zama gargadi ga jam’iyyar APC cewa babu wata jam’iyya da za ta dauki kanta a matsayin wadda ba za a iya kayar da ita ba

Source: Facebook
Sadiq Gombe ya kara da cewa:
“Alama ce ta gargadi ga jam’iyyar da ke mulki cewa ba su da kariya daga kayar da su. Za a kayar da su."
Shugaban ya kara da cewa wannan zabe ya kara da tabbatar da cewa 'yan Najeriya suna da niyyar zaben dukkanin wadanda suka ga ya fi cancanta.
APC ta yi magan a kan zaben Osun
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi magana kan abubuwan da suka jawo mata rashin nasara a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.
Farouk Aliyu ya ce wasu mambobin jam’iyyar sun ki yin aiki tukuru saboda ba su ji dadin dan takarar da aka zaba ba, kuma hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin jawo matsaloli da dama.
Hakazalika ya bayyana rashin nasarar a matsayin gargadi ga jam'iyyar APC gabanin babban zaben 2027 wanda zai ba ta damar zage damtse wajen ganin cewa an gyara kura-kuran kafin lokaci ya yi.
Asali: Legit.ng

