Yakin Iran Ya Shafawa Trump Kashin Kaji, Farin Jininsa Ya Ragu Sosai a Amurka

Yakin Iran Ya Shafawa Trump Kashin Kaji, Farin Jininsa Ya Ragu Sosai a Amurka

  • Amincewar jama'ar Amurka da Shugaba Donald Trump ta koma kashi 33 cikin 100, mafi ƙanƙanta tun bayan komawarsa Fadar White House
  • Kuri'ar da Reuters/Ipsos ta ba jama'a suka kada ta nuna cewa kashi 64 cikin 100 na Amurkawa ba sa amincewa da yadda Trump ke gudanar da mulkinsa
  • A daya bangaren kuma, kashi 80 cikin 100 na waɗanda aka yi wa tambayoyin sun ce suna ganin yaƙin Amurka da Iran zai ɗauki dogon lokaci kafin ya zo karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Amincewar jama'ar Amurka da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ta ragu zuwa kashi 33 cikin 100, matakin da ya zama mafi ƙanƙanta tun bayan da ya fara wa’adinsa na biyu.

Binciken da aka gudanar na tsawon kwanaki huɗu kuma aka kammala ranar Litinin ya nuna cewa kashi 64 cikin 100 na waɗanda aka yi wa tambayoyin ba su amince da yadda Trump ke gudanar da aikinsa a Fadar White House ba.

Kara karanta wannan

Martanin Obi ga masu karyata ikirarinsa na wa'adi 1 a mulkin Najeriya

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Reuters ta ce farin jinin Trump ya ragu daga kashi 35 cikin 100 da aka samu a wani bincike da aka kammala a farkon wannan watan.

Wannan sabon matakin ya yi daidai da mafi ƙanƙantar amincewar da Trump ya samu a wa’adinsa na farko, wanda ya kai kashi 33 cikin 100 a watan Disamba 2017.

Yaƙin Iran ya rage farin jinin Trump

Rahoton ya nuna cewa farin jinin Trump ya fuskanci koma baya musamman bayan da ya bayar da umarnin kai hare-hare kan Iran tare da Isra’ila.

Yaƙin ya shafi kusan kashi 1 cikin 5 na kasuwancin man fetur na duniya, lamarin da ya haifar da tashin farashin man fetur kuma ya ƙara wa 'yan Amurka matsin tattalin arziki.

Trump ya yi kamfen ne bisa alkawarin rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma guje wa yaƙe-yaƙen da za su ɗauki dogon lokaci.

Da farko dai ya yi iƙirarin cewa rikicin Iran zai ɗauki makonni kaɗan, amma Iran ta ci gaba da nuna ƙarfi, yayin da zirga-zirgar man fetur ta mashigar Hormuz ta ci gaba da fuskantar cikas.

Kara karanta wannan

EFCC ta kai wani mutum kotu kan zargin baba kere da N56m na kudin aikin hajji

Al Jazeera ta wallafa cewa rahoton ya nuna cewa kashi 80 cikin 100 na Amurkawa suna ganin shigar Amurka cikin yaƙin Iran zai ɗauki dogon lokaci.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump zai shiga jirgi ya yi tafiya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun fargabar zaɓe a Amurka

Damuwar da ake da ita kan yaƙin Iran da tashin farashin man fetur na ƙara jefa ‘yan Republican cikin fargaba yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin kare rinjayenta a Majalisar Wakilan Amurka a zaɓen tsakiyar wa’adi da za a gudanar a ranar 3 ga Nuwamba.

A gefe guda, ‘yan Democrat na ganin cewa suna da damar kwace rinjayen majalisar dattawa saboda yakin da Trump ke yi da Iran.

Binciken na baya-bayan nan ya nuna cewa kashi 38 cikin 100 sun ce Democrat ce za ta fi iya tafiyar da tattalin arziki, yayin da kashi 35 cikin 100 suka zaɓi Republican.

Batun harba nukiliya Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohuwar ‘yar Majalisar Wakilan Amurka, Marjorie Taylor Greene, ta yi zargin cewa wasu jami’an gwamnatin Trump suna tattaunawa kan yiwuwar amfani da makaman nukiliya a kan Iran.

Shugaban 'yan Iran a kungiyar NIAC, Jamal Abdi, ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin Iran kafin rikicin ya haifar da ƙarin bala’o’i, ciki har da yiwuwar amfani da makaman nukiliya.

Abdi ya ce yiwuwar amfani da makaman nukiliya a Iran abu ne mai matuƙar tayar da hankali, yana mai gargadin cewa hakan na iya jefa rayuka da dama cikin haɗari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng