ASUU: Mu na kokarin mu yi maza, mu kammala tattaunawa da gwamnati

ASUU: Mu na kokarin mu yi maza, mu kammala tattaunawa da gwamnati

- ASUU ta ce za ta iya koma wa bakin aiki da zarar an biya su hakkokinsu

- Wani shugaban kungiyar Malaman, Ade Adejumo ya bayyana haka dazu

- Farfesan ya fadi abubuwan da su ka sa dole ASUU ta tafi dogon yajin aiki

Bayan kimanin watanni bakwai da rufe jami’o’in gwamnati a Najeriya, Daily Trust ta rahoto kungiyar ASUU ta na maganar bude makarantu.

Malaman jami’a sun bayyana shirinsu na komawa aiki muddin gwamnatin tarayya ta biya su bashin albashin wata da watanni da aka hana su.

Shugaban kungiyar ASUU na reshen Ibadan, Farfesa Ade Adejumo ya bayyana shirinsu na bude makarantu a lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida.

KU KARANTA: Yajin-aiki: Sai inda karfinmu ya kare - ASUU ga Buhari

Kamar yadda rahotanni su ka shaida, Ade Adejumo ya zanta da manema labarai ne a ranar Laraba a babban dakin taron sashen fasaha na jami’ar Ibadan.

Farfesa Adejumo ya ce duk da su na zama da gwamnatin tarayya domin a samu mafita, an hana malaman jami’a albashin watanni da alawus dinsu.

Sauran jagororin ASUU da su ka halarci taron sun hada da Moyosore Ajao, Ayo Akinwole, Femi Abanikanda, Biodun Olaniran da kuma Dauda Adesola.

Wakilan na ASUU sun fito ne daga jamo’in Unilorin, UI, Unisoun, LAUTECH da KWASU.

KU KARANTA: An yi taro an gama babu mafita tsakanin ASUU da Gwamnati

ASUU: Mu na kokarin mu yi maza, mu kammala tattaunawa da gwamnati
Taron ASUU da Gwamnati Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Farfesa Moyo Ajao shi ne ya wakilci Farfesa Ade Adejumo a zaman na yau. Ajao ya ce dole ce ta sa kungiyar ASUU ta tafi yajin-aiki a watan Maris.

Ya ce: “ASUU ta na yajin-aiki ne domin dawo da martabar jami’o’i. ASUU ta na yajin-aiki ne saboda ‘ya ‘yanta da ke karbar mafi karancin albashi.”

Kwanaki an rahoto Ministan ilmi ya na fadawa Malaman Jami’a su koma gona idan aiki ya gaza, Ministan ya ce dole sai ta IPPIS za a biya Malaman albashi.

Malaman Jami’a da ke yajin aiki a Najeriya sun dura kan Ministan ilmin, sun yi masa raddi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel