Bai kamata Gwamnatin baya ta shiga yarjejeniyar N1.3tr da ASUU ba inji Adamu Adamu

Bai kamata Gwamnatin baya ta shiga yarjejeniyar N1.3tr da ASUU ba inji Adamu Adamu

- Ministan ilmi ya ce alkawarin da aka yi wa Jami’o’i a baya ya jawo matsala

- Adamu Adamu ya bayyana cewa kwanan nan ASUU za ta a janye yajin-aiki

- A lokacin mulkin PDP ne gwamnatin tarayya ta yi wa ASUU alkawarin N1.3t

Punch ta rahoto ministan ilmi, Adamu Adamu ya na zargin gwamnatocin baya da laifin yajin-aikin da kungiyar malaman jami’o’i su ke yi a Najeriya.

Malam Adamu Adamu bai kama sunan gwamnatin da alhakin yajin-aikin ya ke kanta ba, amma ya yi tir da shiga yarjejeniyar N1.3tr da kungiyar malaman.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da wani matashi ya yi masa tambaya a taron da aka shirya da matasa a Bauchi a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba.

KU KARANTA: Abin da ya hana ASUU janye aiki har yanzu

Ya ce: “Abin da ya jawo yajin-aikin ya ki kare wa shi ne gwamnati ta zauna da kungiyar ASUU, ta yarda cewa za ta biya jami’o’i Naira tiriliyan 1.3”

Adamu Adamu ya ce: “Na yi imani cewa lokacin da su ke sa hannu a yarjejeniyar, sun san cewa ba zai yiwu su cika alkawarin da su ka dauka ba.”

Ministan ilmin ya nuna cewa tun da gwamnati ta sa hannu, yarjejeniyar ta tabbata, duk da kuwa gwamnati ba ta da inda za ta fito da wadannan kudi.

Da ya ke bada amsa, Ministan tarayyar ya nuna takaici game da halin da yajin-aikin ya jefa makarantu, ya yi alkawarin cewa an kusa koma wa aiki.

KU KARANTA: Saura kiris ASUU ta janye yajin-aiki inji Ministan kwadago

Bai kamata Gwamnatin baya ta amince da bukatun ASUU ba inji Adamu Adamu
Kungiyar ASUU da Gwamnti Hoto: Punch.ng
Asali: Twitter

“Ba mu jin dadi da aka rufe makarantunmu, ba mu jin dadin yadda aka jagwagwala tsarin lokacin karatu. Amma laifin gwamnatin da ta sa hannu ne.”

Ministan ya yi albishir da cewa: “Ina tabbatar maku, mu na daf da cin ma matsaya, kuma nan ba da dadewa ba, za mu cin ma matsaya da su (ASUU).”

A makon jiya karamin ministan ilmi ya fito ya na cewa ASUU ta na bata lokaci ne kawai da yajin-aiki domin 80% na Malamai sun shiga tsarin IPPIS.

Ministan ya caccaki Malaman Jami’a, amma kungiyar ASUU ta yi maza ta yi raddi, ta karyata shi. A halin an yi watanni 7, an gaza shawo kan Malaman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng