Gaskiyar dalilin da yasa ba za mu iya biya wa ASUU bukatarta ba - Ngige

Gaskiyar dalilin da yasa ba za mu iya biya wa ASUU bukatarta ba - Ngige

- Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta a kan bukatar malaman jami'a ta ASUU

- Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa ba za su iya biyan kudi naira biliyan 110 da ASUU ta nema na gyara jami'o'i ba

- Ya ce hakan ya kasance ne saboda halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu sakamakon annobar korona

Ministan kwadago da daukar ma’aikata, Chris Ngige, ya ce gwamnati ba za ta iya biyan bukatar kungiyar malaman jami’a ta ASUU ba saboda halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

ASUU na neman a bata naira biliyan 10 domin farfadi da makarantun jami’a.

Ngige, ya bayyana hakan ne a daren ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawar sirrin da mambobin kungiyar ASUU a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Dan Najeriya ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai a Amurka

Gaskiyar dalilin da yasa ba za mu iya biya wa ASUU bukatarta ba - Ngige
Gaskiyar dalilin da yasa ba za mu iya biya wa ASUU bukatarta ba - Ngige Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta gabatar da cewar naira biliyan 20 kawai za ta iya bayarwa.

“Gwamnati bata adawa da gyare-gyaren amma wannan gwamnatin ta ce saboda halin da tattalin arziki ke ciki, sakamakon COVID-19, ba za mu iya biyan naira biliyan 110 ba wanda suka nema nag yare-gyaren,” in ji ministan.

KU KARANTA KUMA: An yi rikici tsakanin 'yan majalisa da shugaban INEC wurin bayanin kasafin kudi

A gefe guda mun ji cewa, bayan kimanin watanni bakwai da rufe jami’o’in gwamnati a Najeriya, Daily Trust ta rahoto kungiyar ASUU ta na maganar bude makarantu.

Malaman jami’a sun bayyana shirinsu na komawa aiki muddin gwamnatin tarayya ta biya su bashin albashin wata da watanni da aka hana su.

Shugaban kungiyar ASUU na reshen Ibadan, Farfesa Ade Adejumo ya bayyana shirinsu na bude makarantu a lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel