ASUU ta gano kadarorin Akawun Gwamnati, kungiya ta bukaci AGF ya yi bayani
- Kungiyar ASUU ta ce ta bankado wasu dukiyoyin AGF a boye a jihar Kano
- Shugaban ASUU na yankin Bauchi, Lawan Abubakar ne ya bayyana haka
- ASUU ta ce Ahmed Idris ya kashe biliyoyi wajen sayen kasuwa da wani otel
Kungiyar malaman jami’a, ASUU, ta nemi Akawun gwamnatin Najeriya, Ahmed Idris ya fito ya fadi yadda ya mallaki wasu kadarori na biliyoyi.
Shugaban ASUU na shiyyar Bauchi, Farfesa Lawan Abubakar, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2020.
Kungiyar ta na so Ahmed Idris ya yi karin-haske a game da yadda ya saye wani otel a kan Naira miliyan 500, ya ruguza otel din ya kama gina shago.
KU KARANTA: Yajin-aiki: Tawagar Gwamnati za ta yi zama da Shugabannin ASUU
Kamar yadda Farfesa Lawan Abubakar ya bayyana, yanzu haka ana tsakiyar wannan katafaren aiki. Jaridar Daily Nigerian ta fitar da wannan rahoto.
ASUU ba ta tsaya nan ba, ta ce ta bankado AGF din ya biya makudan kudi ya sayi kasuwar kayan masarufi da canjin kudi da ke garin Gezawa, Kano.
Lawan Abubakar ya na zargin cewa an batar da biliyoyi wajen fansar wannan kasuwa. Shugaban na ASUU ya bukaci ‘yan jarida su taya su bincike.
Ya ce: “Na farko shi ne ayi bincike a gano wanene ya saye Sokoto Hotel a Kano, a kan N500m, ya biya kudi, sannan ya shiga rushe otel din washegari, ya na gina katafaren shago.”
KU KARANTA: ASUU: An gaza shawo kan Malaman Jami'a da ke yajin-aiki
“Ta ya ya, kuma ta ina ya samu kudin da zai yi wannan aiki?”
“Aiki na biyu shi ne a tayamu bankado wanene a boye ya ke zuba kudi a kasuwar kaya ta Gezawa da canjin kudi."
Jaridar ta ce Ahmed Idris bai iya daukar wayarta domin kare kansa daga zargin malaman Jami’an da ke yajin aiki tun cikin watan Maris ba.
A baya kun ji cewa kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta gabatar da UTAS a gaban gwamnatin tarayya, a matsayin madadin manhajar nan ta IPPIS.
Ana sa ran cewa za a gabatar da UTAS a gaban AGF, NITDA, da NSA domin a amince da manhajar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng