Gwamnati ta gaza shawo kan Kungiyar ASUU kan yadda za a biya N30bn
- Ba a cin ma matsaya ba a zaman Kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya
- Ministan kwadago ya yarda za a biya Malaman albashi da alawus ta IPPIS
- Shugaban kungiyar ASUU ya ce fau-fau ba za su shiga cikin manhajar ba
Jaridar Punch ta ce bangarorin biyu sun samu sabani a game da hanyar da za a bi wajen biyan malaman jami’a bashin albashi da alawus dinsu.
Gwamnati ta na so ta biya malaman da ke yajin-aiki albashin da aka hana su da kuma alawus din EAA ta manhajar IPPIS da ASUU ta ke adawa da ita.
KU KARANTA: Kungiya ta roki Zulum da Matawalle su sa baki kan yajin-aikin ASUU
Kungiyar malaman jami’ar a karkashin shugabanta, Farfesa Biodun Ogunyemi ta hakikance a kan cewa malamai ba za su yi rajista da manhajar ba.
Charles Akpan wanda ke magana da yawun bakin ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, ya shaida wa ‘yan jarida an dage zaman sai ranar Litinin.
Mista Akpan ya ce dakatar da zaman da aka yi, zai ba ‘ya ‘yan kungiyar ASUU su zauna su yanke shawara game da yadda za a biya su wadannan kudi.
Ana sa ran cewa za a cigaba da zama a ranar 26 ga watan Oktoba domin shawo kan yajin-aikin.
KU KARANTA: ASUU ta yi magana game da yajin-aikin Jami'o'i
Gwamnati ta amince ta biya Naira biliyan 40 da malaman jami’a su ke bi bashi a matsayin alawus din karin aikin da su ka yi tun Nuwamban 2019.
Daga cikin wannan kudi, gwamnatin tarayya za ta soma bada Naira biiliyan kafin 6 ga Nuwamba.
Idan za ku tuna, kun ji cewa za a biya sauran kudin daga baya, sannan za a saki N20bn a farkon 2021, za ayi amfani da kudin wajen bunkasa jami’o’i.
An tsaida wannan magana ne a domin kawo karshen yajin-aikin da ASUU ta dade ta na yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng