ASUU: Gwamnatin Tarayya ba ta cika duka alkawuran da mu ka yi da ita ba
- Kungiyar Malaman Jami’a ta yi magana game da yajin-aikin da ta ke yi
- Shugaban ASUU ya ce gwamnati ba ta cika duka alkawuran da ta yi ba
- Biodun Ogunyemi ya karyata ikirarin da Minista ya yi na shawo kansu
Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta ce sam ba a kai ga matakin karshe na janye dogon yajin-aikin da ake ta faman yi a jami’o’in gwamnati ba.
Jaridar Vanguard ta rahoto kungiyar ta na cin-karo da ministan kwadago, Dr. Chris Ngige, wanda ya fito ya na nuna yajin-aikin ya kusa zuwa karshe.
A cewar Chris Ngige, an biya wa ASUU shida daga cikin bukatu tara da ta gabatar wa gwamnati.
KU KARANTA: Sai inda karfinmu ya kare a kan makarantun Jami’a - ASUU
Da ya ke hira da Vanguard a ranar 15 ga watan Nuwamba, shugaban kungiyar ASUU, Biodun Ogunyemi ya ce gwamnati ba ta cika alkawuranta ba.
Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce: “A iyaka saninmu, babu abin da aka yi wa mutanenmu, kuma ba mu son alkawuran bogi.”
Shugaban ASUU na kasa ya ce: “Bari mu dauki batutuwan daya bayan daya.”
“Albashinmu da aka hana na watanni hudu zuwa takwas, su na nan har yau ba a biya ba. Da an biya, da mun ji. Haka maganar alawus din karin aikin koyarwa.”
KU KARANTA: ASUU: Gwamna Zulum da Bello Matawalle su sa baki
“Ba a kai ga kafa kwamitin ziyara a jami’o’i ba, idan da an yi hakan, da ‘Yan Najeriya sun ji sunayen wadanda aka zaba kamar yadda gwamnati ta sanar.”
“Ba a duba lamarin kutsen da gwamnatocin jihohi su ke yi wa jami’o’i ba. Ba a koma kan batun sake duba yarjejeniyar 2009 ba.” Inji Farfesa Biodun Ogunyemi.
Shugaban kungiyar ya kuma ce ba a fara dabbakar da yarjejeniyar 2019 ba. Bayan haka kungiyar ta zargi gwamnati da bude mata shafin bogi a dandalin Twitter.
Ana so ya zama sai masu takardun digiri mai kyawu ne za su rike koyar wa a makarantu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng