Gwamnatin Buhari ta na neman ta yi mana horo da yunwa inji kungiyar ASUU

Gwamnatin Buhari ta na neman ta yi mana horo da yunwa inji kungiyar ASUU

- Kungiyar ta ce har yanzu babu maganar komawa bakin-aiki a Jami’o’i

- ASUU ta na cewa sai an biya bukatunta sannan za ta janye yajin-aikin

- Shugaban ASUU na shiyyar Neja-Delta ya zargi Gwamnati da zalunci

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a a Najeriya ta ce ba za ta dakatar da yajin-aikin da ta ke yi ba, jaridar Daily Trust ta rahoto wannan a ranar Alhamis da dare.

ASUU ta ce za ta cigaba da yajin-aikinta har sai gwamnatin tarayya ta saurari kokenta da kyau.

Malaman jami’ar sun zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da hana su albashinsu domin ayi masu hora da yunwa saboda sun ki na’am da IPPIS.

KU KARANTA: Ba za mu taba na'am da IPPIS ba - ASUU

Da ya ke magana da ‘yan jarida jim kadan bayan taron kungiyar a Jami’ar Neja-Delta, jihar Bayelsa, shugaban ASUU na yankin ya bayyana wannan.

Farfesa Uzo Onyebiama ya yi kira ga matasa da iyayen yara su ba su goyon-baya a fafatukar da su ke yi, a cewarsa domin ganin an gyara jami’o’in kasar.

Uzo Onyebiama ya ce ba don karon kansu su ka tafi yajin-aiki ba, ya ce manufarsu a gyara ilmi.

Farfesa Onyebiama ya zanta da ‘yan jarida ne dazu tare da shugaban ASUU na jami’ar NDU.

KU KARANTA: Taron ASUU da Gwamnati bai haifar da 'Da mai ido ba

Gwamnatin Buhari ta na neman ta yi mana horo da yunwa inji kungiyar ASUU
Taron kungiyar ASUU Hoto: Punchng.com
Asali: Twitter

Sauran wadanda su ka halarci taron manema labaran sun hada da shugaban ASUU na Jami’ar Otouke, Austen Sado da Dr. Kingdom Tonbara na UNIPORT.

“IPPIS ta zama makamin datse karfin ikon jami’o’i daga hannun shugabanninta, ta karbe masu karfin da aka ba su bayan sun yi fafatuka.” Inji Onyebiama.

Kungiyar ta ce: “Za mu cigaba da wannan fafatuka, sai an saurari kukanmu daidai gwargwado.”

A kwanakin baya kun ji cewa kungiyar ASUU ta fadi abin da zai hana Malaman jami'a koma wa aiki har yau, kungiyar ta ce ta na kokarin a koma karatu.

ASUU ta ce za ta iya koma wa bakin aiki da zarar gwamnati ta biya su duk wasu hakkokinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng