ASUU za ta koma tebur da Gwamnati gobe domin kawo karshen yajin-aiki
- A ranar Juma’a Malaman Jami’a za su koma zama da Gwamnatin Tarayya
- Kungiyar ASUU ta shafe fiye da watanni takwas ta na yajin-aiki a Najeriya
- Zuwa gobe da safe za aji yadda tattaunawar ASUU da Gwamnati za ta kaya
Jaridar This Day ta fitar da rahoto cewa wata babbar tawaga ta gwamnatin tarayya za ta gana da shugabannin kungiyar malaman jami’a, ASUU.
Bangaren gwamnatin tarayya za su yi zama da kungiyar ASUU ne a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020, da nufin ganin karshen yajin-aiki.
Mataimakin darektan yada labarai na ma’aikatar kwadago, Charles Akpan, ya bada sanarwar wannan zama da gwamnati za ta yi da malaman jami’a.
KU KARANTA: Gwamnati za ta kai ASUU kotu
Kamar yadda Mista Charles Akpan ya bayyana, za ayi zaman ne da karfe 11:00 a dakin taron ma’aikatar.
Bangaren gwamnati bai yi karin-haske game da batutuwan da za a tattauna game da su ba, amma ana sa ran cewa ayi kokarin ganin an bude makarantu.
Chris Ngige da sauran wakilan gwamnatin tarayya za su yi bakin kokarinsu na ganin ASUU ta janye dogon yajin-aikin da ta shafe wata da watanni ta na yi.
Jaridar ta ce a zaman da aka yi na karshe, gwamnati ta fada wa malaman jami’ar cewa ba ta da kudin da su ke sa ran za su samu bayan alawus dinsu.
KU KARANTA: Buhari ya yarda ya biya Malaman Jami'a alawus
Ministan kwadago, Ngige ya nuna cewa abin da za su iya ba ASUU ba zai zarce Naira biliyan 40 ba, sai kuma Naira biliyan 20 na gyaran jami’o’in kasar.
A halin yanzu kungiyar ta fara koka wa game da yadda tattaunawarsu da gwamnati ya ke daukar lokaci, malaman sun zargi gwamnati da yaudarar jama’a.
Kwanakin baya kun ji yadda Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Malaman Jami’a su rungumi noma, wannan maganar ba ta yi wa kungiyar ASUU dadi ba.
Ministan ilmi ya ce gwamnati ba ta rike malaman jami'a ba, don haka za su iya ajiye aikinsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng