Isa Ashiru Ya ba 'Yan Najeriya Shawarar Abin da Za Su Koya daga Zaben Osun
- Isa Ashiru Kudan ya yaba wa al’ummar Osun kan yadda suka tsaya kai da fata wajen sake zaben Gwamna Ademola Adeleke
- Dan takarar gwamnan na jam'iyyar ADC a jihar Kaduna ya bukaci ‘yan Najeriya su zabi jam’iyyar a 2027 da ake tunkara
- Isa Ashiru Kudan ya ce sakamakon zaben gwamnan jihar Osun ya nuna amannar da ‘yan Najeriya suka yi ga dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna – Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Isa Mohammed Ashiru, ya yaba wa al’ummar Osun bisa kare wa gwamna Ademola Adeleke kuri’unsu har ya sake lashe zabe.
Isa Ashiru Kudan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi irin hakan a babban zaben 2027 da ke tafe, ta hanyar zabar ADC a matsayin jam’iyyar da za su marawa baya a fadin kasar.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abdulwaheed Olayinka Adubi, kakakin yakin neman zaben Isa Ashiru Kudan ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.
Dan takarar gwamnan ya taya Gwamna Ademola Adeleke murnar sake lashe zabe a karo na biyu domin ci gaba da jagorantar al'ummar jihar Osu.
Isa Ashiru Kudan ya ce sakamakon zaben Osun da aka kammala ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na da cikakken imani da tsarin dimokuradiyya.
Isa Ashiru ya yaba wa masu zabe
Sanarwar ta yaba wa masu kada kuri’a a Osun da suka tsaya tsayin daka tare da kare kuri’unsu cikin jarumtaka.
“Zaben Osun ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki a kasar, tare da yabawa shugabannin adawa kan kudurinsu na hada kai a jihar.” In ji shi.
Dalilin sake zaben Gwamna Adeleke
Isa Ashiru ya ce Adeleke ya cancanci sabuwar dama ne saboda jajircewarsa wajen yi wa al’umma aiki, tausayawa bukatunsu da kuma karfin ayyukan da ya gudanar da nasarorin da ya samu a Osun.
Gwamna Ademola Adeleke dai ya samu nasara ne a zaben na ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026, bayan ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji.
Adeleke, wanda ya tsaya takara karkashin Accord Party, ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.
Dan takarar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180.

Source: Facebook
APC ta yi watsi da sakamakon zaben Osun
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin yakin neman zaben gwamnan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.
Kwamitin yakin zaben ya bayyana cewa Gwamna Ademola Adeleke bai samu mafi yawan ingantattun kuri’un da aka kada ba.
Jam'iyyar ta ce ba ta amince da sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi ba, kuma ta fara duba kayayyakin zaben kafin ta yanke shawarar matakin da za ta dauka.
Asali: Legit.ng

