Gwamna Zulum da Bello Matawalle su shiga cikin rikicin ASUU inji NPG da NYF

Gwamna Zulum da Bello Matawalle su shiga cikin rikicin ASUU inji NPG da NYF

- National Professional Group da Northern Nigerian Youths Frontiers sun koka da yajin-aikin ASUU

- Kungiyoyin sun bukaci gwamnonin Zamfara da Borno su sa baki domin a dawo karantarwa a Najeriya

Wasu kungiyoyin matasa masu suna National Professional Group da Northern Nigerian Youths Frontiers, sun sa baki game da lamarin yajin-aikin ASUU.

Wadannan kungiyoyi biyu sun yi kira ga shugabannin Najeriya su yi kokarin sasanta kungiyar ASUU ta malaman jami’ar kasar da kuma gwamnatin tarayya.

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a ranar Lahadi lokacin da su ka zauna da ‘yan jarida a Kaduna.

KU KARANTA: An samu wasu Miyagu sun bindige Malamin Jami’a a Abuja

Mai magana da yawun kungiyoyin, Mustafa Gwarzo, ya bukaci musamman gwamnonin jihohin Zamfara da Borno, su sa baki domin ganin an bude jami’o’i.

Gwarzo ya na so Bello Matawalle da Babagana Zulum su zauna da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari Bello Matawalle da Babagana Zulum.

Malam Gwarzo ya ce bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, sun yanke shawarar wadannan gwamnonin jihohin su sa labule da shugaban kasa.

“Gwamnonin nan biyu sun yi suna, ana ganin darajarsu, saboda shugabancin da su ka nuna, musamman game da abin da ya shafi talaka.” Inji Gwarzo.

KU KARANTA: ASUU ta bayyana inda aka kwana a kan batun yajin-aiki

Gwamna Zulum da Bello Matawalle su shiga cikin rikicin ASUU inji NPG da NYF
Shugabanni ASUU a Aso Villa Hoto: TVC
Asali: Twitter

Kakakin ya ke cewa; “Dalibai sun gaji da zama a gida, yaran talakawa su na wahala yayin da wasu su ka zama tantiran shu’umai saboda dogon yajin aikin.”

Ya ce: “Wannan zanga-zanga da ake yi a fadin kasar nan, a sanadiyyar zaman banza da takaicin da ke damun matasan Najeriya ne, babu abin da su ke yi.”

Kwanakin baya kun ji yadda shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya maidawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari martani a kan batun IPPIS.

Biodun Ogunyemi ya ce Kungiyar ASUU za ta tashi ta kare Jami’o’i iya bakin karfinta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel