Arewa
Ko shakka babu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, ma'abota dandalan sada zumunta sun yi musayar ra'ayoyi dangane da wannan shawara da gwamnan jihar Bauchi ya yanke ta fitowa cikin shirin fim din na Up North.
Hukumar'yan sanda ta samu nasarar cafke wannan shu'umin mutum tare da hadi gwiwar reshen ta na garin Anka, inda ta gudanar da wani sintiri tare da ran-gadi har na tsawon sa'o'i hudu da har sai da hakar ta ta cimma ruwa.
Sarkin ya bayyana hakan yayin da shugaban kasar ya kai ziyarar jajantawa al'ummar jihar dangane da ibtila'in ruwan sama da ya afku a kwanakin baya da ya salwantar da rayukan mutane 11 da kuma dukiya ta kimanin naira biliyan 2.3.
Hukumar a reshen ta dake birnin Maiduguri, ta gurfanar da tsohon ministan ne tare da wasu mutane hudu a gaban babbar kotun tarayya dake babban birnin Damaturu na jihar Yobe bisa aikata laifin almundahanar makudan dukiya.
Tsohon shugaban kasa Obasanjo da mataimakin sa Atiku Abubakar sun hadu yau, Laraba, a Abuja a wurin wani taro da cibiyar Gusau ta shirya a wani Otal. Tun bayan da suka bar mulki, Atiku da Obasanjo basa ga maciji balle batun cigaba
A cewar sa tuni kamfani mai rike da kwangilar wannan aiki, Julius Berger Plc, ya fara aikin gadan-gadan a sassa uku na hanyar babu kakkautawa, inda ya kara da cewa gwamnati ta kudiri inganta duk wani nakasun gine-gine a kasar nan.
A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kalubalanci masu zargin sa kan cewar ya yi shiru ya sanya idanu kurum kan kashe-kashen da makiyaya ke faman aiwatar wa cikin wasu sassa na kasar nan ta Najeriya.
Kwamandan hukumar na jihar, Mista Babangida Dutsinma, ya sanar da hakan a jiya, Talata, yayin wata ganawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN). Ya kara da cewar, kafin hukumar su ta samu labarin abinda yak e faruwa
Hukumar 'yan sanda ta jihar Jigawa, ta tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a duniya cikin dokar wani daji dake karamar hukumar Dutse ta jihar kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito a ranar Talatar da gabata.
Arewa
Samu kari