Abin Tausayi: Matashin da Ya Auri Mata 2 Rana 1 Ya Rasu a Wani Yanayi Mai Cike da Al'ajabi
- Matashin nan da aka ta yadawa lokacin da ya auri mata biyu a rana guda, ya rasu a cikin wani yanayi da aka bayyana a matsayin abin al’ajabi
- An ce Yusuf Jamiu Itopa ya fadi ne a lokacin da yake biyan kudin tagis da ya saya a garin Okene da ke jihar Kogi
- Iyalansa sun ce har yanzu ba a gano musabbabin rasuwarsa ba duk da gwaje-gwajen da aka yi masa a asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Matashin nan dan jihar Kogi, Yusuf Jamiu Itopa, wanda ya ja hankalin jama’a a kafafen sada zumunta watannin baya bayan ya auri mata biyu a rana guda, ya rasu.
Rahotanni sun nuna cewa matashin ya rasu a cikin wani yanayi da iyalansa da shaidu suka bayyana a matsayin abin al’ajabi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan shafukan da mutum zai shiga domin samun tallafin N50,000

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa Yusuf Itopa, wanda aka fi sani da lakabin “Pharmacist” duk da cewa ya kammala karatun kimiyyar kwamfuta, dan asalin Ozuma, Okengwe, ne da ke Karamar Hukumar Okene a Jihar Kogi.
Rahotanni sun ce ya rasu ne a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba, 2026, a unguwar Okengwe Ehi, watanni bayan bikin aurensa na musamman ya dauki hankalin jama’a a kafafen sada zumunta.
Yadda matashin ya fadi a kasuwa
Wani dan uwan mamacin, Haruna Surajudeen, ya ce yana tare da Itopa a ranar da ta gabaci rasuwarsa, lokacin da mamacin ya shaida masa cewa mahaifinsa ya tura masa kudi domin sayen tayils.
A cewar Surajudeen, Yusuf ya gaya masa cewa zai je Okene washegari domin sayen kayan ginin.
Ya ce da misalin karfe 10 na safe a ranar Asabar ne ya samu kiran waya cewa Yusuf Itopa ya fadi kwatsam yayin da yake sayen tayils a Okene.
Wani ganau mai suna Usman Idris, wanda ya ba dan uwan mamacin labarin abin da ya faru, ya ce Yusuf Itopa ya fadi ne a daidai lokacin da zai biya kudin kayan da ya saya.
Idris ya ce mamacin ya zauna ba tare da ya ce uffan ba, sannan kafin ya ankara, sai ya fara faduwa, lamarin da ya sa ya yi gaggawar rike shi.
Ya ce daga nan ne ya tare babur mai kafa uku domin kai shi wani asibiti da ke kusa, wato Iruvochinomi General Hospital, inda aka sanya masa iskar oxygen nan take.
A cewar bayanin, daga baya aka mayar da mamacin zuwa Reference Hospital da ke Okene, bayan wani dan uwansa ya iso asibitin farko kuma ya gano cewa har yanzu likita bai duba shi ba.
An kasa gano musabbabin rasuwarsa
Ya ce mamacin ya fara zufa, lamarin da ya sa suka yi tunanin cewa yanayinsa na inganta, sai dai kwatsam halin da yake ciki ya sauya zuwa yanayi muni.
Ya ce:
“Sai ya fara zubar da jini daga bakinsa. Dukkanmu mun yi mamaki. Likitan ya tambaya ko maciji ne ya sare shi, amma na gaya musu babu wani abu makamancin haka. Tun lokacin da aka kawo shi asibitin, bai yi magana ba.”
Surajudeen ya kara da cewa sakamakon gwaje-gwajen da aka yi wa mamacin bai nuna wata matsala ba, lamarin da ya sa ma’aikatan lafiya suka kasa gano musabbabin halin da yake ciki.
An tsinci gawar magidanci a Taraba
Kun ji cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da gano gawar wani magidanci dan shekara 30, Haruna Ishaka a yankin karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba.
Wasu majiyoyi da suka san yadda lamarin ya faru sun yi zargin cewa mutumin ya aamu sabani da matarsa sakamakon neman matan da ake zargin mijin yana yi.
Asali: Legit.ng

