Akwai Rigima: Gwamnan APC da Kotu Ta Kwace Takararsa Ya Sha Sabon Alwashi

Akwai Rigima: Gwamnan APC da Kotu Ta Kwace Takararsa Ya Sha Sabon Alwashi

  • Hope Uzodimma ya ce babu wanda zai karɓi tikitin takarar sanatan APC da yake riƙe da shi ya ba wani mutum
  • Gwamnan ya buƙaci mazauna Imo su yi wa APC kamfen, yana mai cewa ba za su goyi bayan wata jam'iyya ba
  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta cire sunan Uzodimma daga takarar sanatan Imo ta Yamma tare da maye gurbinsa da Rochas Okorocha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Imo - Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ƙaryata hasashen cewa zai iya rasa tikitin takarar sanata da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ba shi.

Uzodimma ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026 bayan halartar ibadar coci a ɗakin ibada na fadar gwamnatin jihar da ke Owerri, babban birnin Imo.

Uzodinma ya sha alwashi kan takararsa
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Gwamnan ya ce duk wanda ke yaɗa labarin cewa za a karɓi tikitin daga hannunsa a ba wani mutum yana yaudarar jama'a ne, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bayyana abin da Tinubu yake tsoro kan zaben 2027

“Idan wani ya gaya muku cewa zan riƙe wannan tikitin, amma wani ya karɓe shi ya ba wani mutum, ku gaya masa cewa ƙarya ne.” In ji shi.

Uzodimma ya bukaci a yi wa APC kamfen

Gwamnan ya kuma buƙaci mazauna jihar da su fita su yi wa APC kamfen gabanin zaɓukan da ke tafe.

Ya bayyana cewa ɓangarensa na siyasa ba zai goyi bayan wata jam'iyya ba, yana mai jaddada cewa APC ce kaɗai za su mara wa baya.

A kalamansa:

“Ku je ku yi wa jam'iyyarmu kamfen, babbar jam'iyyarmu ta All Progressives Congress (APC). Babu wata jam'iyyar siyasa da za mu bi.”

Uzodimma ya kuma bayyana 'yan takarar APC da yake son mazauna jihar su zaɓa a zaɓukan majalisun dokoki masu zuwa.

“A zaɓen majalisar dokokin jiha, APC ce. A zaɓen majalisar wakilai ma, APC ce.” In ji shi.

Dangane da takarar sanata, ya ambaci Patrick Ndubueze a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a yankin Okigwe. Ya ce shi ne ɗan takarar sanata a yankin Orlu, yayin da Alex Mbata zai wakilci yankin Owerri.

Kara karanta wannan

Amaechi ya hango abin da zai haddasa yakin basasa a Najeriya ana batun zaben 2027

Abin da kotu ta yanke kan tikitin

Martanin gwamnan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta cire sunan Uzodimma a matsayin ɗan takarar APC na sanatan Imo ta Yamma.

Kotun ta kuma umarci hukumar da ta maye gurbinsa da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

Mai shari'a Obiora Egwuatu, wanda ya jagoranci zaman kotun, ya bayyana cewa Okorocha ne ya samu mafi yawan ƙuri'u a zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar ranar 18 ga Mayun 2026.

Alƙalin ya soki INEC kan amincewa da takarar Uzodimma, duk da abin da ya kira “gagarumar hujjoji na takardu da ke nuna cewa gwamnan bai lashe zaɓen fitar da gwani ba”.

Okorocha, wanda ya mulki Imo daga 2011 zuwa 2019, ya shigar da ƙara a watan Agustan 2026 yana ƙalubalantar amincewar INEC da Uzodimma a matsayin ɗan takarar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Wike ya tsage gaskiya kan rawar da ya taka wajen soke takarar gwamnan APC a 2027

Okorocha ya yaba da hukuncin kotu

Bayan hukuncin, Okorocha ya bayyana shi a matsayin nasara ga mazauna yankin Imo ta Yamma.

Ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu, yana mai iƙirarin cewa fadar shugaban ƙasa ba ta ƙara goyon bayan yadda ake tafiyar da al'amuran siyasa a Jihar Imo ba.

Uzodinma ya ce ba zai bar takararsa ba
Gwamna Hope Uzodinma na Imo zaune a ofis Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Batun akwai hannun Wike a soke takarar Hope

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya musanta cewa yana da hannu a hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke amincewa da takarar Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma.

Ministan​ na babban birnin tarayya Abuja ya kira zarge-zargen da ake yi masa da cewa ƙoƙari ne na ɓata masa suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng