Sheikh Murtala Assada Ya Yi Zazzafar Magana kan Tallafin N50,000 da Aka Fara Turawa Yan Najeriya
- Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Asaba ya yi zazzafan martani kan tallafin N50,000 da gwammatin tarayya ke bayarwa
- Malamin ya nuna takaicinsa kan yadda talakawan Arewa ke murna da wannan tallafi duk da ukubar da suke fuskanta sakamakon matsalar tsaro
- Ya kuma ccacaki gwamnatin tarayya kan rashin magance matsalar tsaro a Arewa, inda ya yi kira ga al'umma su farka daga barci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Fitaccen malamin addinin Musulunci mazaunin jihar Sakkwato, Sheikh Mustala Asada ya soki tallafin N50,000 da gwamnatin tarayya ta fara tura wa mutane.
Malamin ya nuan damuwa kan halin da ake ciki game da matsalar tsaro, yana mai bayyana yadda yan ta'adda ke cin zarafin mata da wulakanta mutane musamman a Arewa.

Source: Facebook
Sheikh Assada ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumuns, wanda ATP Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.
Malamin ya bayyana cewa gwamnati ta shekara hudu ba tare da magance matsalar tsaro ba, amma da zabe ya gabato ta kirkiro shirin tallafin N50,000.
Ya kuma soki talakawa masu murna da tallafin, yana mai cewa an shekara hudu na cin mutuncin iyayensu a hare-haren yan bindiga, amma sun zo sun farin ciki da wasu yan kudi da aka ba su.
Murtala Asada ya ce:
"A shekaru hudu ana mulki, ana kama iyayenku ana ci musu mutunci, a kama mahaifinka, ka bada kudi amma karshe a harbe shi a turo muku gawarsa, amm wai a ce za a baka N50,000 kuma ka zo kana murna saboda ƙasƙanci.
"Wai kuma ka ga talaka a Arewa yana murna wai gwmanatin tarayya ta ba shi tallafin N50,000, abin takaici, muna rokon Allah Ya karya wannan gwamnati."
Malamin ya tunawa mutane cewa a ranar gobe kiyama, kowa zai amsa tambayoyi kan kiwon da aka ba shi a anan duniya.
Sheikh Asada ya ce abin bakin ciki ne yadda ke kashe mutane a Arewacin Najeriya ba tare da gwamnatin tarayya ta dauki tsauraran matakai don magance matsalar ba.
Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su dawo cikin hayyacinsu, su yi abin da ya dace, yana mai cewa gwamnatin tarayya da Shugaban Kasa hankalinsu ya tashi.
Ya ce tarukan da yan adawa suka yi a Sakkwato da Kebbi sun tada wa shugaban kasa hankali, yana mi cewa hakan wa'azi ne ga duk wani dan siyasa.
Asali: Legit.ng

