Tsohon Abokin Takarar Buhari Ya Bayyana Dalilin Kin Karbar Tayin Mukamin da Tinubu Ya Yi Masa
- Fasto Tunde Bakare ya ce ya ƙi tayin Shugaba Bola Tinubu na naɗa shi minista saboda yana ganin ya tsufa da nauyin da ke tattare da muƙamin
- Ya bayyana cewa ya fi son taimaka wa gwamnati ta hanyar ba da shawarwari da samar da hanyoyin magance matsalolin ƙasa
- Bakare ya jaddada cewa ba ya cikin ’yan adawa, kuma har yanzu cikakken ɗan jam’iyyar APC ne da zai kada ƙuri’a idan lokacin zaɓe ya zo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Leicester - Shugaban Cocin Citadel Global Community Church, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana dalilin da ya sa ya ƙi tayin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na naɗa shi minista a gwamnatinsa.
Faston ya ce ya ƙi karɓar muƙamin ne saboda yana ganin ya tsufa da ɗaukar nauyin da ke tattare da aikin minista.

Source: Twitter
Dalilin da ya sa Bakare ya ƙi zama minista
Malamin addinin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026 yayin wani taro da ƙungiyar Envoy Nation ta shirya a birnin Leicester da ke ƙasar Birtaniya, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Maimakon shiga cikin majalisar ministocin shugaban ƙasar, Bakare ya ce ya fi son taimaka wa gwamnati daga bayan fage ta hanyar ba da shawarwari da kuma gabatar da hanyoyin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Ya ce ya sanar da Tinubu cewa duk da cewa ba ya sha'awar shiga majalisar ministocinsa, a shirye yake ya bayar da gudummawa wajen ci gaban Najeriya ta hanyar shawarwari masu amfani a duk lokacin da ake buƙatarsa.
Ya ce ba ya cikin ’yan adawa
Bakare ya kuma fayyace cewa shawarar da ya yanke na kasancewa a wajen gwamnati ba tana nufin yana adawa da gwamnatin Tinubu ba.
Ya jaddada cewa bai taɓa kasancewa cikin ’yan adawa ba, yana mai bayyana kansa a matsayin mutum mai bayar da shawarwari kan yadda za a inganta harkokin mulki.
Faston ya ce zai ci gaba da bayyana ra'ayinsa a duk lokacin da ya lura da wani abu da bai dace ba a manufofi ko matakan da gwamnati ke ɗauka.
Sai dai ya bayyana cewa ba wai kawai sukar gwamnati yake yi ba, domin yana kuma ƙoƙarin gabatar da hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin da ya gano.
A kalamansa:
"Na gaya wa Tinubu cewa na tsufa da zama minista, amma zan taimaka daga bayan fage ta kowace hanya da nake ganin za ta amfani ƙasata.
“Ban taɓa kasancewa cikin ’yan adawa ba. Ni mutum ne mai bayar da shawarwari. Idan na ga wani abu ba daidai ba, zan gabatar da hanyar magance shi.”
Bakare ya tabbatar da kasancewa ɗan APC
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya kuma sake jaddada cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jaridar TheCable ta kawo labarin.
Ya yi watsi da tunanin cewa zai iya sauya sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa wata cikin sauƙi, yana mai cewa ba ya sauya goyon bayan siyasa a kai a kai.
“Ba zan iya sauya sheƙa cikin gaggawa ba, na shiga wata jam’iyya yau, sannan gobe in koma wata. Ni cikakken ɗan APC ne, kuma zan kaɗa ƙuri’a idan lokacin zaɓe ya zo.” In ji shi.
Jawaban Bakare sun nuna cewa ya fi son bayar da gudummawa ga harkokin mulki ta hanyar shawarwari na sirri da kuma sukar manufofin da yake ganin ba su dace ba, maimakon riƙe wani muƙami a gwamnatin Tinubu.

Source: Facebook
Tunde Bakare ya so ya gaji Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin Citadel Global Church, Pastor Tunde Bakare, ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban kasar Najeriya.
Malamin addinin ya bayyana cewa idan ya samu dama, ya so ya gaji shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki.
Asali: Legit.ng


