An kama hadimin Sule Lamido da kayan zabe da kudi, hotuna

An kama hadimin Sule Lamido da kayan zabe da kudi, hotuna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa ta cafke Mansur Ahmed, mai taimaka wa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a bangaren kafafen sadarwar zamani. Jami’an rundunar ‘yan sandan sun kama shi ne da kayan aikin zabe da kudi.

‘Yan sanda sun kama Mansur, fitaccen dan gani-kashenin jam’iyyar PDP, a kan hanyar sa ta zuwa kauyen Chiyako a karamar hukumar Birnin Kudu. ‘Yan sandan sun kama shi ne yayin da su ke gudanar da aikin su.

An kama hadimin Sule Lamido da kayan zabe da kudi, hotuna
Hadimin Sule Lamido da kayan zabe da kudi
Asali: Facebook

An kama hadimin Sule Lamido da kayan zabe da kudi, hotuna
Mansur Ahmed
Asali: Facebook

An kama hadimin Sule Lamido da kayan zabe da kudi, hotuna
Hadimin Sule Lamido da aka kama da kayan zabe da kudi
Asali: Facebook

An samu Mansur, dan asalin karamar hukumar Jahun, da kayayyakin zabe da su ka hada da huluna, takardun hukumar zabe ta kasa (INEC), jaket din ma’aikatan INEC, kudi, shaidar ma su sa-ido a zabe (observers), lmbobin mota da sauran su.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: Ma’aikatan INEC biyu sun gudu da sakamakon zabe a Katsina

Mansur na dauke da dukkan wadannan kayayyaki ne domin ya samu damar shiga wuraren gudanar da zabe amma sai dubun sa ta cika bayan ya fada hannun jami'an ‘yan sanda yayin da suke gudanar da aikin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel