Dauke Wuta: Minista Ya Bayyana Halin da Ake Ciki kan Gyaran Lantarki a Najeriya

Dauke Wuta: Minista Ya Bayyana Halin da Ake Ciki kan Gyaran Lantarki a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ce an dawo da wutar lantarki a yankuna da dama da matsalar ta shafa a jihohin Legas, Ogun, Oyo, Kwara da Abuja
  • An gyara layin wutar lantarki na Benin-Egbin mai ƙarfin 330kV da aka lalata, wanda ya taimaka wajen ƙara wutar da ake kaiwa Legas
  • Minista Joseph Tegbe ya ce wutar da ake kaiwa yankin Legas ta haura megawatt 1,000, yayin da ake ci gaba da gyara sauran wuraren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa an dawo da wutar lantarki a yankuna da dama na jihohin Legas, Ogun, Oyo, Kwara da Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan matsalolin da suka haddasa katsewar wutar a baya-bayan nan.

Tegbe ya kuma ce gwamnati ta kammala gyaran layin wutar lantarki na Benin-Egbin mai ƙarfin 330kV, wanda wasu mutane suka lalata, tare da dawo da shi aiki domin jigilar wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar tsaigaita wuta da Boko Haram

An gyara wuta a Najeriya
Ministan wutar lantarki a Najeriya, Joseph Tegbe Hoto: Joseph Olansunkanmi Tegbe
Source: Instagram

Gwamnati ta sanar da dawo da wutar lantarki

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026 inda ya bayar da bayani kan matakan da gwamnati ta ɗauka domin magance matsalar.

Ya ce an riga an dawo da wutar lantarki a yawancin wuraren da matsalar ta shafa, yayin da jami'an da abin ya shafa ke ci gaba da ƙoƙarin dawo da cikakkiyar wutar lantarki a sauran yankuna.

A cewarsa, ma'aikatan da ke aikin gyaran sun mayar da hankali wajen tabbatar da cewa dukkan wuraren da matsalar ta shafa sun samu wutar lantarki kamar yadda ya kamata.

An gyara layin Benin-Egbin mai ƙarfin 330kV

Tegbe ya bayyana cewa gyaran layin wutar lantarki na Benin-Egbin mai ƙarfin 330kV da aka lalata ya taimaka sosai wajen ƙara yawan wutar da ake kaiwa yankin Legas.

Ya ce bayan kammala gyaran, an dawo da layin cikin tsarin jigilar wutar lantarki, lamarin da ya taimaka wajen mayar da wutar da ake kaiwa yankin Legas zuwa yadda take kafin aukuwar matsalar.

Kara karanta wannan

Ta'addancin 'yan bindiga ya ritsa da sojoji da mai juna biyu a Taraba

Ministan ya ce yanzu jimillar wutar lantarki da ake kaiwa yankin Legas ta haura megawatt 1,000, wanda ya taimaka wajen daidaita yanayin samar da wutar lantarki a yankin.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da aiki domin tabbatar da cewa sauran wuraren da har yanzu ba su samu cikakkiyar wutar lantarki ba sun amfana da gyaran da ake yi.

Gwamnati ta haɗa kai da kamfanonin wutar lantarki

Ministan ya ce gwamnatin tarayya na aiki tare da manyan masu ruwa da tsaki a ɓangaren wutar lantarki domin tabbatar da dorewar samar da wuta da kuma inganta yadda ake rarraba ta ga 'yan Najeriya.

Ya lissafa kamfanonin samar da wutar lantarki, masu kula da tsarin sarrafa wutar, Kamfanin Kula da Layukan Wutar Lantarki da kamfanonin rarraba wuta cikin waɗanda ke taimakawa wajen wannan aiki.

A cewarsa, haɗin gwiwar waɗannan hukumomi da kamfanoni na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa ana samun ingantacciyar wutar lantarki a sassa daban-daban na ƙasar.

Tegbe ya jaddada cewa babban burin gwamnatin tarayya shi ne samar wa 'yan Najeriya wutar lantarki mai inganci da za a iya dogaro da ita a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado haramtacciyar matatar mai ta 'yan kasar waje cikin daji

An dawo da wuta a Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja, Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Batun karin kudin wuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi martani kan jita-jitar da ake yadawa kan shirin ƙara kuɗin wuta.

Gwamnatin ta jaddada cewa ba ta da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki a faɗin Najeriya, kamar yadda ministan wutar lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng