Bisa sharadi daya ne kawai PDP za ta shiga zabe a Jigawa, in ji Sule Lamido

Bisa sharadi daya ne kawai PDP za ta shiga zabe a Jigawa, in ji Sule Lamido

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Jigawa ta ce ba lallai ta shiga zaben gwamnoni da za a yi a ranar 9 ga watan Maris ba matukar ba a dauke kwamishinan rundunar ‘yan sanda, Bala Senchi, daga jihar ba.

Jam’iyyar ta yi zargin cewar an yi amfani da jami’an ‘yan sanda wajen aikata magudi da razana ‘yan jam’iyyar adawa yayin zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

Mustapha Sule Lamido, kayayyen dan takarar kujerar sanatan jigawa ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a daren jiya, Laraba, a gidan Radiyon Freedom. Mustapha da ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido.

Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe dukkan kujerun ‘yan majalisar dattijai da wakilai a zaben da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Bisa sharadi daya ne kawai PDP za ta shiga zabe a Jigawa, in ji Sule Lamido
Mustapha Sule Lamido
Asali: Twitter

Mustapha, wanda aka fi kira da ‘San Turaki’ ya sha kaye a hannun sanatan yankin mai ci, Muhammad Sabo Nagudu. Mustapha ya samu kuri’u 143,611 yayin da Nakudu ya samu kuri’u 224,543.

Mustapha ya ce APC ta yi nasara a zaben ne saboda jami’an ‘yan sanda da ragowar jami’an tsaro sun goyi bayan jam’iyyar yauin zabe.

Ya ce ‘yan sanda sun raka jagororin APC zuwa mazabu inda su ke dukan ‘yan jam’iyyar adawa tare da sayen kuri’u’.

DUBA WANNAN: Ali Nuhu da jerin wasu fitattun jarumai da su ka taya Buhari murnar cin zabe

Za mu kauracewa zaben idan har kwamishinan ‘yan sanda, Bala Senchi, ya cigaba da zama a jihar saboda ya riga ya nuna kan sa a matsayin mai goyon bayan APC.

“Babu dalilin cigaba da zaman sa a jihar tunda an riga an yi masa canjin wurin aiki,” a cewar Mustapha.

A ranar 6 ga watan Fabrairu ne babban sifeton rundunar ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya yi canjin wurin aiki ga wasu manyan jami’an ‘yan sanda.

Senchi na daga cikin manyan jami’an ‘yan sanda da canjin ya shafa. Sai dai magajin sa, Rabiu Ladodo, da aka turo jihar har yanzu bai zo ya karbi aiki ba, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewar akwai siyasa a ciki.

Da aka tuntubi Audu Jinjiri, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ya ki cewa komai a kan wannan batu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel