Zargin sayen kuri'a: Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin fitar da miliyan 233

Zargin sayen kuri'a: Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin fitar da miliyan 233

A yau Alhamis ne gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da ware zunzurutun kudi Naira Miliyan 233.5 sai dai ta karyata rahotanin da ke cewa an fitar da kudin ne domin sayan kuri'u a zaben gwamna na jihar da za a maimaita.

A yayin da ya yi hira da manema labarai a ofishinsa, Kwamishinan Kananan hukumomi, Murtala Garo ya ce an fitar da kudin ne domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a kananan hukumomi da ake bitansu a yanzu.

Ya ce jita-jitar ba gaskiya bane inda ya kallubalanci masu yada jita-jitar da su tafi su duba yadda za a kashe kudaden wurin gudanar da ayyuka ga al'ummar jihar Kano har ma ya bayar da misali da ayyukan da ake yi a na kananan hukumomin.

DUBA WANNAN: Zaben gwamoni: Akwai ayar tambaya a kan gaskiyar Buhari - Dan majalisar Kano

Zargin sayen kuri'a: Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin fitar da miliyan 233
Zargin sayen kuri'a: Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin fitar da miliyan 233
Asali: Twitter

"Ka san yadda siyasa ya ke, ba ka raba shi da zargi nan da can. Ba kuri'u za a saya da wannan kudin ba. An ciro kudin ne domin wasu ayyuka da gwamnati za ta gudanar a garuruwan.

"Misali akwai wasu kananan hukumomi cikin 13 da za ayi wa aiki kuma ba su cikin wadanda za a sake zabensu kamar Tsanyawa, Kabo da sauransu. Sai dai wadanda ke yada jita-jitan sun ce wai mun cire kudin ne domin sayan kuri'u.

"Ina kallubalantar kowa har ma da manema labarai su tafi wuraren da aka ce za a gudanar da ayyukan su ga abinda ke faruwa. Za ku ga ayyukan da akeyi," inji Garo.

Kwamishinan ya kara da cewa, "gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ba ta kawo siyasa wurin yiwa mutane ayyuka.

"Za a gudanar da wadannan ayyukan ne domin amfanin talakawa, mene za sa a jefa siyasa cikin sa. Tsaftatacen gwamnati muka gudanarwa karkashin mulkin Ganduje," inji Garo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel