An Nada Alkalai 375 domin Sauraron Kara bayan Zaben 2027

An Nada Alkalai 375 domin Sauraron Kara bayan Zaben 2027

  • An rantsar da alƙalai 375 a ranar Litinin domin su yi aiki a kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen da za su biyo bayan 2027 a faɗin Najeriya
  • Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ce 138 daga cikin alƙalan sun taɓa aiki a irin waɗannan kotuna
  • Ta buƙaci alƙalan su yi adalci, su mutunta kundin tsarin mulki tare da tabbatar da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Yayin da ya rage kwanaki 68 a gudanar da babban zaɓen shekarar 2027, an rantsar da alƙalai 375 da za su saurari ƙararrakin zaɓen da ’yan takara da jam’iyyun siyasa za su shigar a faɗin Najeriya.

An gudanar da bikin rantsar da alƙalan ne a ranar Litinin a Abuja, inda shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta bayyana muhimmancin aikin da aka ɗora masu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta ragargaji APC kan hukuncin rusa takarar Atiku a kotu

Zaben da aka yi a Anambra
Wajen da aka yi zabe a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Abin da tsarin mulki ya tanada

Vanguard ta rahoto cewa sashe na 285(1) da (2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bai wa shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara alhakin kafa kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe.

Waɗannan kotuna za su saurari rikice-rikicen da suka shafi zaɓen Gwamnoni da na ’yan majalisun tarayya da na jihohi.

Haka kuma, Sashe na 134(3)(a) da (b) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanadi lokacin kafa kotunan da kuma buɗe ofisoshinsu domin karɓar ƙararraki.

Alƙalai 138 sun taɓa aikin a baya

A jawabinta, Mai Shari’a Dongban-Mensem ta bayyana cewa an zaɓi alƙalan ne daga kotuna da cibiyoyin shari’a daban-daban a faɗin ƙasar.

Ta ce daga cikin alƙalai 375 da aka rantsar, mutum 138 sun taɓa aiki a kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe a baya, yayin da sauran 237 sababbi ne.

Shugabar kotun ta bayyana cewa wannan mataki ya nuna aniyar hukumomin shari’a na kare dimokuraɗiyya, bin doka da kuma tabbatar da ingancin tsarin zaɓen Najeriya.

Kara karanta wannan

An kara wa jami'an INEC albashi da alawus yayin da ake shirin zaben 2027

Ta ce taron yana nuna shirye-shiryen hukumomin shari’a wajen gudanar da ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora musu.

Taswirar FCT, Abuja
Taswirar FCT, Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Mai Shari’a Dongban-Mensem ta bayyana cewa amincewar jama’a ga dimokuraɗiyya ba ta dogara da yadda aka gudanar da zaɓe kaɗai ba, har ma da kasancewar hanyoyin da suka dace na warware rikice-rikicen zaɓe cikin adalci da lokaci.

Kotu ta rusa takarar Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kotun Najeriya ta soke sahihancin zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta ADC a zaɓen 2027.

Hukuncin ya haifar da ƙarin matsalolin shari’a ga jam’iyyar adawa ta ADC, wadda ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan matakin kotun.

A yanzu haka dai ADC na cikin manyan jam’iyyun adawa da ke ƙoƙarin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng