Sakamakon zabe: APC ta zargi Rochas da murde zabin jama’a a jihar Imo
Jam’iyyar APC a jihar Imo ta zargi gwamna Rochas da yin amfani da wasu jami’an tsaro wajen murde sakamakon zaben kujerar gwamna da aka yi a jihar ranar Asabar.
Jam’iyyar ta yi kira ga magoya bayanta da su saka ido a kan kuri’un da su ka kada domin ganin cewar gwamna Rochas bai samu damar murde sakamakon zabe don surukin sa ya zama gwamna ba.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Cif Marcelinus Nlemigbo, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a jihar.
Nlemigbo ya yi kira ga hukumar soji da rundunar ‘yan sanda da su tsawatar wa da jami’an su don kar a yi amfani da su wajen aikata magudin zabe.
Gwamnan Rochas na daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC da su ka ci zaben kujerar majalisar dattijai bayan karewar wa'adin sa na biyu a kujerar gwamna.
Tun a jiya Legit.ng ta wallafa rahoton cewar Ofishin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC dake karamar hukumar Ngor Okpuala na jihar Imo na ci wuta bal-bal a yanzu haka.
Wasu yan baranda ne suka fasa inda ma'aikatan INEC ne hada sakamakon zaben gwamna da yan majalisar dokokin jihar misalin karfe 2 suka tayar da hankali.
DUBA WANNAN: INEC ta bayyana cewar zaben gwamna a Sokoto bai kammalu ba
Wata majiya ta bayyana cewa yan barandan sun fittitike jami'an tsaron da wajen kafin suka bankanwa ofishin wuta.
Da wuri jami'an yan sanda suka kawo agaji ga ma'aikatan hukumar INEC dake Imo da kuma kayayyakin zabe. Shugaban hukumar INEC na jihar Imo, Francis Ezeonu ya ce shikenan an tayar da rigima a unguwar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng